App not Install/ Yanda zaka magance ta!

 

Wane Application ne yaqi budewa a wayar ka?

 Ka karanta wannan Rubutun a Nitse.

  Hanyoyi guda biyu domin magance matsalar installing na application akan waya (Application not installed).


1) ka tabbata baka cika wayar ka da apps da yawa, ta yanda wani application É—in ba zai samu wajen hawa ba, sannan kuma ka tabbata akwai space a  storage naka, ma'ana storage É—in ka akwai waje da É—an yawa bai cika tab ba.


2) ka bawa app ɗin da kake so kayi installing ta cikin sa permission (install unknown apps) permission, misali kana so kayi installing ta cikin Telegram, may be kaga wani app a Telegram kana so ka sauke sa kan wayar ka, to dole sai ka ba wayar ka dama kan cewa ta riƙa installing na app daga Telegram, saboda asali an yi android ne ta rinƙa yin installing na app daga Playstore, to duk wani app wanda ba Playstore ba dole sai ka bashi dama idan kana so kayi installing na wani application ta cikin sa, kamar xender, file manager, WhatsApp, browser, Telegram, da sauran su.


Fatan kun fahimta.


  Duk mai matsalar installing yayi wannan abun guda biyu.


1) ya samar da space a storage nasa.


2) ya bawa waɗannan apps ɗin permission na "install unknown apps" 👇👇


1) ku shiga setting wajen search sai ku rubuta install, sai ku zaɓi "install unknown apps".


2) bayan ka shiga, sai ka nemo inda aka rubuta "install unknown apps" sai ka danna.

3) Zaka ga jerin apps kamar haka.

4) sai ka nemo duk ta inda aka turoma da Application din misali whatsapp, ko telegram, ko facebook sai ka shiga, sai ka kunna nan wajen 👆.


5) Sannan ku nemo file manager ɗin ku, ku shiga shima ku kunna nan 👆.


  Idan ku kayi waÉ—annan abubuwan dana ambata a sama, to zaku iya install É—in app daga Telegram É—in ku da kuma file manager É—in ku da duk ta inda aka turo muku Application bai bude ba.


  Sannan akwai bangren playstore ma shima zamuyi darasi akan sa insha Allah





Previous Post Next Post