Application uku (3) ga duk masu amfani da wayar android ko iphone 2022


 Application uku (3) ga duk masu amfani da wayar android ko iphone 2022.

 Da sunan Allah mai rahma da jinkai mahalaccin dukkan halittu, Tsira da amincin Allah su qara tabbata ga fiyayyen Halitta. 


   Darasin mu na yau akan wadansu Application ne guda uku wanda nayi bincike kwarai da gaske akan su kuma tabbas ana buqatar su domin aikin mu na yau da kullum da wayar hannu.

  Akwai abubuwa da dama da mutane da yawan gaske suna ganin kamar dole sai mutum ya mallaki computer ko wata babbar waya domin suyi amfani da aiki ko hada wani abun.

To yau cikin ikon Allah na kawo mana wadansu application wanda tuntuni na dora videon su ko nace videon da yake da cikakken bayani akan su a youtubr channel din mu na KK Techtube bayan haka zan ajje muku link din videon a kasan wannan rubutun tare da link din kowane Application. 

 Kawai idan ka kalli videon kaje chan kasa domin dakko Applications din. Amman ga wadanda suke buqatar karin bayani akan kowane daga cikin su zasu ga na rubuta Karin bayani to sai su tsaya su karanta domin ganin yanda abin yake.

   KARIN BAYANI.

 Application na farko zai taimaka maka ne wajen rage nauyin hoton ka ko kuma chanja masa format. Format shine kamar hoton yana JGo zaka iya mayar da shi PNg ko JPEG wanda kowannan su akwai yanayin aikin su koda ace kana so kyu amfani da hoton ta wani bangare a website ko editing ko print, bayan nan zaka iya rage masa Mb kuma batare da Qualitin hotin ya ragu ba. Gaskiya wannan application ya zama wajibi ka ajje shi a wayar k domin watar rana.

 Application na biyu: Zai baka damar rage nauyin waka ko karatu batare da karfin sautin ya ragu ba ma'ana Qualiti na saukin wakar ko karatun ya ragu ba saboda akwai lokutan da zakaga dan voice ne ko waka amman yana da Mb da yawa bayan nan kana so k tura ta whatsapp ko ta wani platform. To kaga wannan Application zai taimaka ma. Akwai masuyin prigramming ko kuma amfani da wani website domin haka application na wakoki ko kundi na Al'qur'ani mai girma to wannan zaitaimaka sosai.

 Application na karshe: Shine wanda zai baka damar rage nauyin video kowane kala ne kuma duk nauyin sa a wayar k batare da kayi amfani da wata software ta comouter ba. Sannan zaka iya zabar duk adadin videon a lokachi guda domin rage nauyin su.

 Wadannan Application suna da amfani sosai ga link din su nan a kasa


Link din Application din da zaka rage nauyin Hoto

👇👇👇👇👇👇👇

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.csdeveloper.imgconverter


 Link din Application din da zaka rage nauyin waka ko karatu

👇👇👇👇👇👇👇

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.bdroid.audiomediaconverter



Link din Application din da zaka rage nauyin video

👇👇👇👇👇👇👇👇

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.pandavideocompressor


Ga kuma link din videon domin ganin karin bayani

👇👇👇👇👇👇👇👇👇

https://youtu.be/_X5TgJToQM4

 Nagode kuyi share din rubutun domin karuwar hausawa.

Previous Post Next Post