COMPUTER BATARE DA KOWACE KALAR SOFTWARE BA

 


             WIN+ALT+R For Computer!!

 Saudayawan Gaske mutane suna buqatar sanin irin wadannan sirrika na Computer musamman wajen aiki da ita.

Hakan yasa nai waiwaye akan abinda ya shafi Daukar videon screen na computer ( SCREEN RECORD), Da farko de zan fara bayanin me screen record take nupi sannan sai a karshe nayi bayanin yanda zakayi amfani da shi a Computer.

      SCREENRECORD. 

Hanya ce da zata baka damar recording na screen din Device misali ! Akwai Voice Record sannan akwai screen record, Shi voice record zai baka damar daukar iya muryar da kake magana ko ake magana idan ka kunna a wayar ka ko a Computer. iya wannan ne aikin voice record, Sannan akwai Screen record shi zai baka daman ka dauki muryar waje sannan kuma ya dauki cikin screen din wayar ka da zarar ka danna sa to zai dauki dukkanin ilahirin screen din ka kamar de Screenshort shi screenshort iya hoto zai dauka amman shi screenrecord zai dauki videon acreen din ne ! Koda ace na tsawan awanni zakayi zaiyi maka recoding dinsa.

Akwai Application da yawa na wayar android sannan akwai software da yawa na computer wanda suke bada damar wannan screenrecord din, Inda ace wannan rubutun da nakeyi zan danni screenrecord to zai dinga recording din screen din da kuma maganar da nakeyi.

YANDA AKE SCREENRECORD A COMPUTER BATARE DA SOFTWARE BA.

Akwai sirri kala daban-daban wanda zakaga ana amfani da su a computer batare da software ba wannan yana daya daga cikin su wanda zan kowa.

 Da farko da zarar kanason fara record na screen din computer ka abinda zaka farayi shine.

 Zaka danna WIN+ALT+R a lokachi daya.

WIN shine alamar WINDOWS wanda take a jikin Keybord din computer bayan ka danna sa batare da ka Daga ba zaka dannan ALT a jikin Keybord din ka bayan nan sai ka qara da R acikin jerin kalmomin Keybord dinka duk a lokachi daya batare da ka Daga wani daga cikin su ba.

Inde ka danna Haka shikenan Screen record ya fara acikin Computer ka.

koda Games kake zai dauki wannan games din da kakeyi ko kuma kanason kayi Bayanin wani abu acikin Computer musamman Masu Amfani da kafar Youtube domin koyar da Darasi.


 Wannan shine hanya mafi sauki wajen daukar SCREENRECORD a computer

DAGA/ KkTechtube.Net

Ku ziyarchi Youtube Channel mai suna KK Techtube

Previous Post Next Post