Application da zai magance ma rashin daukar zafin waya da kuma chaji da wuri.

 


Assalamu alaikum!

Wannan Application din zai gyarama wayar ka da kuma kareta daga shan chaji da kuma yawan Daukar zafin da takeyi.

 Da sunan Allah mai Rahma mai jinkai, Yau darasin da mukayi a Youtube akan wani Application ne wanda zai taimakawa wayar ka naganin ta daina daukar zafi da kuma yawan shan chaji da rashin chaji da wuri da kuma hanyoyin da zaka magance wasu matsaloli acikin wayar ka musamman a wannan lokachi na Yanayin zafin gari da akeyi.

Tuntuni na ajje videon a Youtube bayan nan na ajje wannan link din ne domin bamu damar daukar Application din sannan ga wanda baiga videon ba duka zan ajje muku link din videon da kuma Application din achan kasa zakuga koren rubutu bayan nan a saman koren rubutun zakug nayi bayanin link din menene.

Ga wanda yake son karin bayanin akan Application din ya karanta wannan rubutun dukkan sa.

    BAYANI.

Da farko de bayan ka dakko application din zaka bude shi kamar yanda kake bude sabon kowane application.

Bayan ka bude shi zai tambaye ka akan cewa ka Taba Rooting din wayar taka ko baka taba ba ko kuka baka sani ba to shawarar da zan baka shine ka bata rubutun karshe na uku kenan shine I'm not sure baka tabbatar ba kenan, Bayan ka taba zakaga Next a kasan Application din sai ka taba kana tabawa Application din zai bude maka sannan zakayi la'akari da wata alamar (+) a kasan hannun daman ka to sai ka taba bayan ka taba zakga wajen Empty amman idan a lokachin da ka bude Application din kana amfani da wani application kamar irin screen record to zai iya nuna maka shi kadai. To koda bai muna maka ba ko ya nuna maka a kasan zakaga SHOW MORE APP sai ka taba shine zai nuno maka dukkan Application din cikin wayar ka.

Bayan ya nuno maka zaka yi la'akari da da gefen kowane Application zakaga dan wani rubutu a jikin sa inde kaga sunan Application sannan a gefen sa akwai wannan rubutun to yana nuni da cewa wannan Application din yana amfani a bayan wayar ka "Background" kenan to sai ka taba Application din idan kga dama zaka iya mark din su ko guda nawa ne.

bayan nan shine zaka taba wajen add din Application din inyaso ma zaka iya gwadawa daya bayan daya incase saboda gudun samin matsala.

To bayan ka zaba shima zakaga ya ware maka Applications din gida biyu akwai Background fresh da kuma hybernite to zakayi la'akari da kasan kowane Application. Anan ne inde kaga Application a bangaren Background fresh to shikenan batare da ka qara taba shi ba shi wannan application din zai kulle ma shi. Amman idan ka ganshi bangaren Hybernite to lalle wannan application yana buqatar da sai ka ba wadannan Application na bangaren Hybernite hutu to sai ka taba su zakaga wata alama a kasa hannun damar ka da kalmomi uku daya yana kan daya (Zzz) kana tabawa shine zaka bashi damar yayi block na wadannan nan Application din. 

Insha Allah idan kayi haka zak magance matsalar kowane Application da yake aiki a Background dinka.


Ga link din videon kai tsaye zuwa Youtube.

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

Bayan ka kalli videon sannan a kasa ga link din Application din sai ka dakko shi.


Ga link din Application din

👇👇👇👇👇👇👇👇👇

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.oasisfeng.greenify&hl=en&gl=US


Nagode

Previous Post Next Post