Sabon Application wanda dukkan mai amfani da wayar Android ko iphone /2022

 


Sabon Application wanda dukkan mai amfani da wayar Android ko iphone /2022.

 Assalamu alaikum barkan mu da sake saduwa acikin sabon darasin mu na yau.

 Na kawo mana wani Application wanda zai baka damar kayi Extraction na ko wane file a wayar ka ta iphone ko Android bayan nan acikin wannan darasin nayi bayanin yanda zaka iya saita game ta pes2022 wanda tuntuni na rigada na dora videon wannan darasi akan youtube din mu mai suna Kk Techtube. Bayan nan zanyi bayanin extraction domin nasan akwai wanda kalmar bama su san da ita ba koda ace ma an gane kalmar da fassarar ta da yaren turanchi akwai qarin bayanin aikin wannan kalmar a kasa zanyi bayanin insha Allah yanda zaka gane sosai da aikin ta.
  
 EXTRACTION.
 
 Acikin wannan application extraction shine ka yi unzip din file wadanda suke amfani da computer na tabbata sun gane me ake nufi da extraction. Domin inde aka turama Software a computer ko kuma kayi download din ta a wani website din to dole wata software tana buqatar kayi extraction din ta da wata software mai suna Winrar ko kuma wata software daban.

 To haka shima wannan Application din mai suna ZARCHIVER zai baka damar extraction din dukkan wani file da kayi download a internet domin amfani da shi. Misali akwai lokachin da kake so ka bude wani zip na games ko theme na blog ko na wani website. to zakayi amfani da wannan Application din domin ka cire wannan folder din. 

 Bayan nan wannan application din zai taimaka maka ka mayar da ni file ko folder zuwa (zip). Zip shine zaka iya hade duk yawan kayayyakin ka misali Hotunan ka koda sun kai (DUBU). Zaka mayar da su zuwa abu daya sannan bazaiyi nauyi ba. Amman duk lokachin da wanda ka turawa da wannan ZIP din na folder da ka hada dole sai yayi amfani da Extarction sannan zai cire wannan hotunan dukkan su.
  
  AFWA.
Ina neman afwa wajen yin bayanin nasan dukkan wani abu saboda idan aka fito dashi wajen ganewa zaiyiwa mutane wahalar ganewa sai wanda ya nutsu domin fahimtar. Kawai inde kana buqatar ka gane dukkan abinda nake nufi akwai link din videon da nayi cikakken bayani aciki.

 Amman yana da kyu ka karanta dukkan rubutun domin fahimtar inda na dosa. Bayan nan shima link din Application din da kuma na game din PES200 din zan ajje muku achan kasa domin amfani da su duka biyun sannan insha Allah akwai games da yawan gaske wanda zanyi darasi akai saboda nasan akwai masu bibiyata amman suna buqatar suga ina darasi akan games insha Allah zan na yi muku wannan darasi.

 Sannan shi wannan darasin zai taimaka maka koda wace game aka turo maka zaka iya amfani da ZACHIVER kayi amfani da shi.

Ga link din Application din na Android.
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

  Ga link din Application din na iphone
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

 Ga link din PES2022 din
👇👇👇👇👇👇👇👇👇
Pes2022 ina kokarin dora muku insha Allah ku jira

Ga link din videon
👇👇👇👇👇👇

 Kada ku manta da share din wannan website mai albarka domin cigaban Al'umma hausawa a duk inda suke.
Nagode.
Previous Post Next Post