SABUWAR FASAHA 2022 kayi amfani da waya biyu cikin waya daya


 SABUWAR FASAHA 2022.

kayi amfani da wayoyi biyu cikin waya daya!.

 Assalamu alaikum 'yan'uwa barkanmu da sake saduwa acikin sabon darasin namu wanda zanyi muku bayani ne akan wadansu Application guda biyu masu abin mamaki bayan nan kuma akwai amfani sosai a tattare da wadannan Applications din.

Dukkanin su aikin su daya sai de wani yafi rinjaye ta wata hanyar daban saboda akwai ayyuka da yawa game da su (Applications) din.

Da farko de tuntuni na dora video akan Youtube wanda yayi cikakken bayani akan wadannan Applications. Ga wanda ta rigada ya kalli videon na youtube kawai yaje chan kasa zaiga inda na ajje links din Applications din domin fara amfani da su. 

Sannan zan ajje links din videon ga wanda baiga videon ba to zai taba sai ya shiga youtube yaga cikakken videon. Haka zalika zanyi karin bayani a kasa game da ayyukan wadannan Applications saboda haka sai ka danyi kasa kadan zakaga nace karin bayani to sai ka tsaya ka karanta duka.

KARIN BAYANI.

Application din kamar yanda na fada a farkon rubutu na dukkanin su aikin su daya sai de akwai dan banbanchi da kuma sauwake wasu abubuwa a cikin kowanne.

1). Wadannan Applications zasu baka dama kayi amfani da wayoyi ko nace screen din wayoyi biyu acikin waya daya koda. Misali idan kana da waya guda biyu zaka iya amfani da wannan Applications sai ka saka wadansu code to acikin wadda kake so kayi amfani da shi kawai zakaga screen din wayar ya fito a cikin dayan nomal dukkan abinda yake acikin wancan wayar zakagan shi acikin wannan wadda ka saka code din. Yana da abin mamaki sosai.

2). Bayan nan daya daga cikin aikin wadannan Applications din shine zakaga iya Cast na dukkan wani applications da kake bude video zuwa TV din ka. 

MISALI.

 Mun sani akwai hanyoyin da zaka bi domin yin kallo da TV bayan ka hada wayar ka ta hanyar amfani da USB cable ko kuma Memory ko Flash wanda ake zuba finafinai. To akwai lokachin da kallon wani videon zai riskeka kuma baka da daya daga cikin wadannan abubuwan da na lissafa domin ganin cewa ka hada wayar ka da TV din da kake so kayi amfani koda kuwa kana da iyalai. To shi wannan Application ko nace wadannan Applications zasu baka damar Cast din dukkan wani video ko App wanda ake iya kallon video a cikin sa batare da kayi amfani da USB cable ba kwai kana danna wani abu acikin Applications din zai kama maka TV din gidan naka kuma zai fito a cikin TV din batare da wani shan wuya ba.

3). Sannan akwai abinda ya danganchi PC bi ma'ana Computer itama wadannan Applications zasu baka damar fito da dukkan abinda ya danganchi wayar ka acikin Computer ka.

Abin kamar Tsafi sai ma ka kalli videon sannan kayi amfani da shi.

Saboda haka zan ajje muku links din kowane acikin sai kuyi download din su bayan nan achan karshe zan ajje links din Videon domin wanda yake buqatar ganin cikakken bayani.


Ga link Application na farko.

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.apowersoft.mirror

Ga link din Application na biyu.

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.apowersoft.mirror.tv

Ga link din Videon.

👇👇👇👇👇👇👇

https://youtu.be/g3dehGML43k

Previous Post Next Post