Yanda zaka sami number america kyuta kayi amfani da ita


   YANDA ZAKA SAMI NUMBER AMERICA KYAUTA (free) KAYI AMFANI DA ITA CIKI HARDA BUDE WHATSAPP! 2022

 Bismillahir rahmanirrahim. Darasin mu na yau shine yanda zaka iya mallakar number kasar waje kowace kasa kake buqata ciki harda number america wadda take da wuyar samu. 
 
  Sauda yawa ansha yimin maganar wannan hanya domin akwai wadanda suke da buqata koda bangaren samin wata number wadda ake iya amsar kiran waya da kuma tura sako da karbar sako. Wannan hanya ce mai wuyar gaske amman cikin ikon Allah na binciko mana wannan hanya wadda kowa zaiyi amfani da ita.
  Tun asali na dora videon akan youtube channel din mu mai suna KK Techtube bayan nan zan ajje muku link din videon dana application din domin kallon videon da kuma sauke application din a wayar ku ta hannu.
   Kafin na je ga ajje muku link din bari nayi godiya ga dunbun masu bibiyar mu dare da rana da kuma share zuwa ga dukkanin abokanan su domin suma su qaru.

 KARIN BAYANI.
   Zanyi kataitaccen bayani akan application din ga wanda basu ga videon ba amman idan ka riga da ka kalli videon kawai kaje chan kasa zakaga link din Application din domin farayin amfani da shi. Zakaga nace ga link din application din to a kasa da wannan rubutun zakaga koren rubutu sai ka taba zai kaika inda zakayi download na application din.
  Farko shi wannan application bayan ka bude shi zakaga yana yi maka bayani ne game da duk da application din ya kunsa to ankasa zakaga GET START kawai sai ka taba shi amman nima acikin wannan rubutu zan danyi mana tsokaci kan abinda Application din ya kunsa.
 ABINDA YA KUNSA.
   Abinda ya kunsa shine zai baka number waya wadda zakayi amfani da ita sannan ka kira waya da ita bayan nan za'a iya kiran ka da ita sannan zai baka damar turo sako SMS da kuma amsar sako ga wadanda suke da number. Zaka iya yin record na wannan kiran wayar da kake tsakanin ka kaida wanda kukeyin wayar.
Bayan nan idan kana son mallakar wasu numbibi na daban dole su sai ka biya kudi sannan zasu baka ya danganta da wace kasa ka zaba akwai kuma kasar da idan ka zaba kawai COINS ne zaka tara shine zaka yi amfani da wannan number din.
  Dole sai ka bude account a Application din zaka saka Gmail din ka ko kuma SMS na wayar ka saboda koda ka chanja waya zakachi gaba da amfani da shi.  Wannan shine takaitaccen bayani akan wannan Application.
 Idan kanason cikakken bayani kaje ka kalli videon a Youtube din mu wanda na ajje muku link din sa a kasa.
  Nagode.

    Ga link din Application din
👇👇👇👇👇👇👇👇

Ga link din videon domin ganin cikakken bayani akan application din
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
Previous Post Next Post