Application biyu (2) da zaka magance duk wani website mai talla ko application kuma zasu baka damar chanja gari.
Assalamu alaikum barkan mu da sake saduwa a yau a sabon darasin namu!. 'Yan'uwa darasin mu na yau zamu bayani ne dangane da sabbin wasu application guda biyu da zasu baka damar magance duk waya kafa da ake takuramaka da talla aciki kamar website ko application.
MENENE AIKIN KOWANNE DAGA CIKIN SU?
Application ma farko shine zai taimaka maka na gano duk wani application da yake talla aciki sannan zai baka damar cire application din daga wayar ka.
Dukkan wani application da ka bude a wayar ka to shi wannan application din zai bincike shi domin baka damar bincikar sa idan akwai talla aciki.
Application na biyu shine zai baka damar kulle duk wani website da yake da yawan talla a cikin sa musamman irin wadannan website din da ake dakko fina-finai acikin su. Zaku ga tallan dake cikin su yayi yawa.
Kai duk wata manhaja inde zaka shig cikin application din nan zai kulle ma tallan ka kalle shi batare da tallan ba. Sannan zai iya baka damar chanja kasa ko ince Gari domin shiga kowane website batar da wannan website din yasan daga ina ka shige shi ba.
TAYA ZAN DAKKO WANNAN APPLICATION?
Kawai kaje chan kasa zakaga na rubuta DOWNLOAD 1 da kuma DOWNLOAD 2 wannan yana nupin Application na farko shine DOWNLOAD 1 sannan na biyu kuma DOWNLOAD 2 kana tabawa zai baka damar sauke wannan application zuwa wayar ka.
AKWAI VIDEON WANNAN DARASI AKAN YOUTUBE?
Tuntuni na dora videon wannan darasi ga wadanda suke bibiyata a youtube nasan sun riga da sun ga cikakken bayanin wannan darasi. Saboda haka kaima zan ajje maka link din videon a kasa saboda haka kaje chan kasa zakaga nace ga link din videon.
Ga link din su nan a kasa ka taba domin download
NAGODE!