Darasin mu akan wani ko nace wasu application biyu masu maqutar amfani ga duk masu amfani da whatsapp musamman ma wanda basa amfani da Gbghatsapp.
Assalamu alaikum ina muku fatan alkhairi yau kamar wasa mun dauki azumi na 28 ranar juma@ Allah ya karbi ibadun mu ameen.
Yan'uwa darasin mu na yau wasu application ne wanda na binciko mana musamman masu amfani da nomal whatsapp wanda zai magance ma matsalolin da kke fama sa su da yawan gaske. Insha Allah zan lissafa su daya bayan daya da kuma cikakken bayani. Bayan haka zan ajje muku link din videon darasin achn kasa wanda tuntuni na riga da na dorashi akan youtube sannan link din application din guda biyu suma suna chn kasa sai kaje kayi download din su.
Application na farko zai baka damar da idan kana amfani da nomal whatsapp to idan aka turoma message sannan akayi deleted din chat din shi wannan application zai fadama wannan chat din da aka goge sannan zai baka damar sauke duk wani status da abokan ka suka dora zuwa wayar ka sannan ya baka damar dorwa a naka status din. Bugu da qari shi wannan application din zai baka damar turawa duk wata number da ka mallaka sako batare da kaye save din ta ba. Mun sani idan ka sami number mutum kuma saka tura masa da sako dole sai kayi save din number bayan nan ka shiga whatsapp sannan kayi refresh sannan zai baka damar ganin number dai k tura masa sakon da kake so ka tura. Amman shi wannan application din batare da kabi wannan dokoki ba direct zaka tura sakon. cikakken bayanin yana cikin videon sai kaje kasa domin ganin link din sannan ka kalli videon.
Akwai abubuwa da yawa wanda wannan application yake da su kawai na dan fadi wasu daga ciki ne.
Application na biyu kuma na karshe: Application ne da aka kirkire shi domin abinda ya danganchi Autoreply. Autoreply ba kamar yanda muka saba amfani da shi bangaren Gbwhatapp ba ko whatsapp business ba. Su wadannan zasu baka damar ka rubutu wani sako wanda duk wanda ya turoma da chat to wannan whatsapp din zai tura masa da wannan sakon koda wane irin sako aka tura masa. Banbanchin wannan application da sauran wanda na fada muku shine. Shi wannan application zak iya saitawa duk wata kalma da mesage ya shigo da ita to shi wannan application din zai tura masa da sakon da ka ajje a ciki.
MISALI: Zaka iya rubuta HAPPY BIRTHDAY. To duk wani sako da aka turoma acikin sa akwai happy birthday to iya shi kadai zakayiwa reply ba kamar wancan ba sabida wancan kowane message yana tura masa da autoreply wannan kuma ka saita iya kalmar da kake so yayiwa reply. Akwai cikakken bayani acikin videon kaje kasa zakaga link din sa.