Google play sun fitar da Application 3 na musulunchi yanda yafi kowane amfani musamman a wannan watan Ramadan

 



Google play sun fitar da Application 3 na musulunchi yanda yafi kowane amfani musamman a wannan watan Ramadan. Wanda ya kamata duk musulmi ya mallake su.

 Assalamu alaikum ina muku barka da wannan lokachi ya ibada cikin ikon Allah yau mun dauki azumi na 11 kenan Allah ya karba mana baki daya.

 Yau darasin namu ne domin duk abinda ya danganchi musulunchi ne. Play store wanda shine ma'ajiyar ko rumbun ajje Application na wayar android sun fitar da jadawalin Application guda uku wanda ya kamata mu musulmai mu mallakesu musamman acikin wannan watan na Ramadan. Sannan yafi kowane Application karbuwa saboda dalilin abinda yake cikin sa.

 Tuntunia na dora videon wannan darasi na tabbata mutane da yawa sun kalli videon sannan kuma sun rabonta da wadannan Application har sun fara amfani da su . Saboda haka kaima kada a barka a baya ka maza-maza ka dakko naka.

 Zan ajje muku link din Applications din duka guda uku da kuma link din videon achan kasa . Sannan zan danyi dan tsokachi akan kowane application da abin da ya kunsa. Domin musan ayyukan su baki daya dukk nayi cikakken bayani a cikin videona na yau.

 WADANNE APPLICATION NE WANNAN?.

Application ne guda uku da zasu taimakeka musamman a wannan watan na Ramadan da ma bayan ramadan domin iya karatun Al'qurani da addu'o'i da sannanin Alqibla shi yasa google play sula fitar da su domin taya mu murnar shigowar wannan wata mai alfarma.

 Application na farko wanda na fara bayani acikin videon wanda kuma dole daman ya kamata nayi bayani domin Al'qurani ne. Shi kuma al'qurani shine farko a ko ina domin maganar mahaliccin mu ne. Shi wannan Application zai taimaka maka ka iya karanta qur'ani da kuma koyon haruffan sa da hanyoyin da zaka iya haddarsa baki daya bayan nan zaka iya kunne Audio wato sauti domin saurara koda kana aiki ne. Shi yasa suma google din suka fara bayanin wannan muhimmin Application na Al'qur'ani. kuje qasa zaku ga link din sa sai ku sauke.

 Application na biyu shine na Alqibla wanda zai nuna ma duk wata hanya da zaka gane inda gabas take da kuma lokutan sallah. Sau da yawa wani lokachi zaka iya taintar kanka a wani gari ko unguwa sannan kana so kayi sallah amman zaka rasa gane sahihin inda zaka kalla kayi sallah. To dukde da wayar iphone tana zuwa da irin wannan abu na nuna inda gabas take to ga wani application ma wanda zaka dakko shi ya taimaka ma ta wannan hanyar. Shima zan ajje muku link din sa achan kasa sai kuje kuyi download.

 Application na uku kuma na karshe shine bangaren Addua akwai dubunnan adduoi acikin wannan application sannan kowace addua da makamanciyar ta domin saukake maka wajen iyawa. Shi wannan Application salon da yazo da shi yana da abin burgewa wajen koyar da kutane adduoi. Zaka iya karantawa sannan ka saka application din ya fassarama adduar da yaren da yayi fice sannan zaka iya kunna sauti wato audio kenan domin ya karanta ma har ka haddace wannan adduar. Bugu da qari wannan application da addua akwai abubuwa da yawa bayan addua abin da ya danganchi Al'qibla da kuma tasbah da saita lokachin shn ruwa da sahorr da kuma lokutan sallah daidai da location ko nace garin da kake. Saboda haka kawai kaje kasa domin download din waddan nan application masu amfani sannan a chan kasan karshe zan ajje muku link din videom domin ganin cikakken bayanin.

 SHIN BABU NA Iphone ne?.

Aa kowannen su akwai na iphone zaka shiga Appstore domin sauke su amman iya na Android kawai zan ajje muku link din sa.

Nagode kada kunmanta dani acikin adduoin ku bayan amsha Ruwa. Da kuka Nemawa mahaifina gafara wajen ubangijin mu domin ya dade da Rasuwa. Nagode


Danna nan ga Al'qur'an

Danna nan ga Alqibla

Danna nan ga Addua supplication

Danna nan ga Link din videon

Previous Post Next Post