Password generator/ Hanyar samun kowane password.
Assalamu alaikum ina muku fatan alkhairi. Yan'uwa ya ibadah Allah ya karbi ibadun mu ameen Yau munkai azumi na Biyar kenan insha Allah.
'Yan'uwa darasin mu na yau zamuyi bayani akan wadansu application guda biyu wanda ya kamata musan da su domin kwata-kwata boyayyu ne sannan idan nayi bayani ko ka kalli videon bayanin zakayi mamakin yanda suke da amfani amman ba'a taba sanin su ba. To har kullum wannan channel mai albarka tana binciko sabbin abubuwa domin ganin mun waye akan duk wani sabon Fasaha musan da ita.
Tuntuni mun dora darasin wannan application akan youtube din mu domin ganin cikakken bayanin sai kje chan ksa zakaga link din videon ga wadanda basu ga videon ba sai su bude su kalla bayan nan dukka a ksan ma zan ajje muku link din dukkan applications din guda biyu. Sannan zanyi bayanin su daya bayan daya insha Allah a kasan rubutun nan.
Application nanfarko zai baka damar generating na password wanda kake buqata sannan kayi save din sa acikin application din dukkan yawan su idan ka chanja waya zakagansu acikin sa domin akwai Backup da kuma Restore. Zai baka yanayin duk wani password wanda zakayi amfani da shi kaje ksa zakaga link din videon domin cikkken bayani.
Application na biyu wani babban application ne da zo a wannan zamin mai abin mamaki wanda zai fitar da duk ruwan da ya shiga cikin speaker din wayar ka. Da zarar wayar ka ruwa ya taba ta kana nunanin ruwa ya shiga cikin speaker to da zarar ka shiga cikin application din ka dannan start dukka ruwan da yake ciki zai fita.
Wadannan Application suna da matuqar amfani.
TAYAYA ZAN DOWNLOAD DIN SU?
A kasa zakaga nace DOWNLOAD 1 shine application na farko DOWNLOAD 2 shine application na biyu sannan a kasa zakaga nace ga link din videon idan kana buqatar kallon videon kenan.
NAGODE.