Wasu application da na binciko mana / Suna da abin mamaki ku gaggauta mallakar su.
Assalamu alaikum! Barkan munda shan ruwa kkar wasa yau mun kai azumi guda 26 Allah ya karbi ibadun mu ameen.
Yau wasu application guda biyu na binciko mana domin amfanin mu a wayar android. Saboda haka ka gaggauta zuwa chan kasa zakaga link din application din duka guda biyun. Bayan nan tuntuni na ajje link din video a kasa domin wanda bai kalli videon a youtube ba zaka iya danna link din sai ka kalli cikakken bayanin acikin videon.
Da farko de wadannan application din suna da matuqar amfani musamman mu da muke amfani da wayar android sannan wani lokachin muna so mu sami sauki a wayar tamu. Kamar abinda ya danganchi screenshot da kuma Nav bar wadda a kasa zanyi muku bayanin su daya bayan daya insh Allah.
KARIN BAYANIN DUKKAN APPLICATION DIN.
1) Application na farko abinda ya danganchi screenshot ne. Da yawan gaske zakaga kana amfani ko kanayin screenshot a wayar ka amman zakaga sunyi yawa amman ka rasa yanda zakayi da su. Kuyimin afwa fa zakuga inayin bayanin wani iri wallahi saboda azumi ne. gashi kuma an sha ruwa.
A takaice de wannan application zai taimaka mak wajen tantance dukkan wani screenshot da kakeyi a wayar ka zaka iya saita lokachin da wannan application zaiyi aiki a cikin wayar ka. Link din cikakken videon yana kasa.
2) Application na biyu da ywan gaske akwai lokutan da zakaga ana samin matsalar Navbar na wayar android musamman mu masu kananan wayoyi to zaka rasa yanda zaka dinga amfani da Back(baya) idan kana buqatar komawa saboda abin ya lalace. To a baya na nuna muku wani application anda zai fitoma da irin wannan Navbar din domin chi gaba da amfani da shi. To matsalar anan itace shi wancan application din idan navbar din ya ba da matsala to shima application din ba lalle yayi ba. To shi wannan sabon application din zai baka damar amfani da Cusor a wayar taka ba tare da kayi amfani da navbar din taka ba. Cikakken bayanin yana cikin videon wanda na ajje link din sa achan kasa sai ka taba domin kallin videon.
NEMAN ADDUA!.
Dan Allah idan kunsha ruwa ku sakani acikin adduar ku da adduar rahma ga mahaifina da ya rasu da mahaifiya ta wadda muna tare yanzu.
Nagode.
Danna nan ga link application na farko