Bismillahir Rahmanir Rahem.!
Assalamu alaikum warahmatullah ina muku barka da wannan lokachi ya ibadah. Allah ya karbi ibadun mu ameen.
Yau darasin mu yana daya daga cikin masu tsadar da za'a iya cewa ba'a taba koyawa ba koda kuwa an koya sai dai ace kwatan-kwachin sa ne. Domin Applications ne guda biyu da na kawo mana domin wasu ayyuka na boye abinda ya danganchi video da kuma audio sannan zaka iya saitawa a lokachin da kake so wannan application din su fara aiki. Batare da ansan kana yin videon ko audio ba.
Zanyi bayanan su daya bayan daya a kasa amman ka sani da cewa tuntuni na dora videon darasin da nayi cikakken bayanin application din achan kasa tare sa link din dukkanin application da na dayi amfani da shi sai kaje chan kasa domin kallon videon da kuma dakko application din.
Kafin nayi muku karin bayanin application din cikin wannan darasi idan ka kalli videon zaku ga nayi tallan wata channel wadda tayi fice wajen koyar da Fasaha da yaren hausa mai suna ( SHAMSU TECH). Wannan channel ta ban-banta da duk wata channel da kuka sani bayan nan itama tana da website wanda yake bude ko nace baje kolin fasahar sa aciki sai kuje ku bibiyi wannan channel a youtube channel da kuma website mai suna shamsutech.com.ng Nagode.
KARIN BAYANI.
1) Application na farko amfanin sa shine zaka iya saita lokachin da kake so wannan application yayi maka recordin ko daukar murya a lokachin da ka saita ko kuma ka danna bayan nan koda ace wayar taka ta shiga security wannan recording zaichi gaba da yi ne. Amfanin sa shine musamman a wannan lokachi na ramadan kana so ka dauki wani sauti na malaminidan yana karatu to kuma zakaga gurin yana cikowa kafin malamin yazo ko bayan ya gama karatun ko tafserin. To gudun yin hakan zaka iya saita lokachin da wannan application zai fara recording da kuma lokachin da zai daina recording. Batare da ka kunna ko kashe wayar ka ba. Yana da amfani sosai cikakken bayanin yana cikin videon kaje kasa zakaga link din sa.
2) Application na biyu: Shi wannan mai tsadar gaske ne domin zai daukar ma videon duk inda kake so batare da an sani ba. Shima zaka iya saita lokachi da ranar da kake da tabbachin zaka shiga wani taro ko wani guri amman bakason asan kanayin videon. To wayar ka dakan ta zata saita ma duka videos din sannan koda baka shiga camera ba zata yi maka wannan record din.
DANNA NAN KA DAKKO APPLICATION MA FARKO
DANNA NAN KA DAKKO APPLICATION NA BIYU