Yau darasin mu zamu tattauna kan wani website mai matuqar abin ban mamaki domin zai mallaka maka duka dadin message din da kke buqata sannan kayi amfani da shi.
Idan aka ce message ba wai wanda zak turawa abokin ka ko budurwar ka ba aa duk wani sako da ake buqata kayi amfani da shi domin bude wani application ko website shine ake kira da OTP wanda ake turo wasu numbobi ko kuma link wanda zai tabbatar da kai ne mai wannan number.
To abin burgewa da wannan website din shine zai bak adadin numbobi da yawa sannan zai baka zabin wanda kake so kayi amfani da shi sannan duk number daya zaka iya amsar OTP sama da Talatin a lokuta daban-daban.
MENENE AMFANIN WANNAN WEBSITE DIN?.
Amfanin wannan website duk da dai na danyi tsokachi kadan akan shi a farkon rubutun nawa amman zan qara fayyace muku yanda abin yake insha Allah.
Amfanin wannan website din shine wani lokachin kana so ka bude whatsapp ko telegram ko instagram ko wani website ko application amman kuma bak so kayi amfani da asalin number ka wanda ta nan ne zasu turama message dan su tabbatar da kaine kayi kokarin budewa to zaka iya shiga cikin wannan website din su baka number ko nace ka zabi number da kake so kayi amfani da ita sannan ko sun turama da wani code ko link zaka iya shiga wannan website domin ganin wannan abinda suka tura. Duk da dai nayi cikakken bayani akan shi website din acikin video a youtube chnnel dina ga duk wanda bai kalli videon ba zan akje muku link din videon a chan kasa insha Allah domin kallon videon da kuma link din website din wanda direct zaka shiga ta ciki.
YA AKE AMFANI DA SHI WEBSITE DIN?.
Bayan ya budema website din batare da ya buqachi gmail ko password ko username dinka ba kawai zaka shiga ne ka zabi nunber da kake so kayi amfani da ita. Kana gama amfani da ita zaka iya fita sai lokachin da ka qara buqatar hakan. Bashi da wani wuya wajen amfani da shi.
TAYA ZAN GANE LINK DIN VIDEON DA NA WEBSITE DIN?.
Da zarar kaje kasa zaka ga rubutu kore an rubuta VIDEO to da zarar ka taba shine zai kai ka zuwa videon kai tsaye. Sannan zakaga na rubuta WEBSITE shima kana tabawa zai kaika zuwa website din kai tsaye.
Muna godiya ga masu bibiyar mu dare da rana ina muku barka da sallah yan'uwa.
Nagode
WEBSITE