Inde kana amfani da Android ga wasu application guda biyu ka gaggauta dakko so

 

Da sunan Mahalaccina nida iyyayena da dukkan Al'umma da duniya da abinda yake cikin ta Ubangijin sammai da kassai. Tsira da aminchi su tabbata ga fiyayyen halitta Annabin mu Annabin karshe Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi wasallam.
 Darasin mu na yau yan'uwa akan wadansu application ne guda biyu wanda tuntuni wasu sun riga da sun dakko su domin amfanin da suke da shi. Saboda haka kaima kayi kokarin mallakar naka domin amfani da shi. Kaje chan kasa zakaga na ajje link din kowane application tare link din videon da nayi cikakken bayani akan darasin wanda tuntuni yana kan youtube channel dina.
 MENENE AMFANIN WADANNAN APPLICATION?.
 
 Appication ne wanda  zai bak damar amfani da wayar ka ta android batare da wayar ka application sun cika maka waya ba. Koda kowa sun cika maka waya zaka iya rage nauyin MB din kowane application da yake acikin wayar ka. Sannan zai baka damar Backup da restore. Abinda hakan yake nufi shine zak iya ajje duk wani application a kan wayar ka koda ka dakko shi daga playstore sannan bayan ka chanja waya zaka iya dawowa dashi cikin wayar ka batare da kasha wuyar neman sa ba. 
 BAYANIN KOWANE DAGA CIKIN SU.
 Application ma farko shine zai baka damar rage nauyin dukkan nauyin kowane MB na application koda kuwa yana da nauyin 100MB zaka iya mayar dashi bai wuce irin 2mb ko 1mb ba sannan kayi amfani da shi.
 
 DALILIN DA YASA ZAKAYI AMFANI DA SHI A WAYA.
 Akwai dalilan da yakamata kayi amfani da wannan application din amman zan dan fada muku wasu daga ciki. Da farko de zaka samu saukin amfani da wayar ka ta daina makalewa sannan zaka sayi guri (space) a wayar ka saboda wani lokachin zaka iya zuwa zakayi download na application a playstore zakaga wannan playstore din ya nunoma wasu application da suke da nauyi akan cewa ka cire su daga wayar ka. To zaka iya rage musu Mb. Sannan wani lokachin kana so ka tura application zuwa ga abokan ka ta whatsapp ko wani chatting amman zakaga wannan application din MB yayi yawa to zaka iya rage nauyin sa tare da amfani da wannan application.

Application na biyu shine zai taimaka maka gurin ajje dukkan wani application akan wayar ka. Daga yau ka sani dukkan wani application da ka dakko shi daga playstore baya zauniya akan wayar ka illa iyaka kawai zakayi amfani da shi ne da zarar kuma ka cire shi a wayar ka zaka neme shi ka rasa sai de ka qara neman sunan shi a playstore sannan ka qara dakko shi. To shi wannan application zai taimaka ma wajen ajje kowane application akan memoryn wayar ka bayan nan idan ka chanja waya zaka iya dawowa da wannan application din batare da ka sha wahalar neman sunan sa ba da kuma download din sa ba. Bugu da qari wannan application zai baka damar cire ko nace Uninstall na adadin duk application din da kake buqata zaka iya makin din application daga Daya zuwa 100 a lokachi daya zannan ka taba Uninstall to dukkan su zasu fita a wayar ka. 

 TAYA ZANYI DOWNLOAD DIN WADANNAN APPLICATION DIN?.
 Achan kasa zakaga nace DOWNLOAD 1 da kuma DOWNLOAD 2 to (Download 1) shine application na farko sannan (Download 2) shine application na biyu. Sannan a kasan su zanyi kokarin ajje muku link din videon idan kuma bansami dama ba sai k ziyarchi Yiutube channel mai suna KK Techtube zakaga videon sai ka kalla.

 Nagode.



Previous Post Next Post