1) Airplane tare da code
Da farko ka fara kunna datar wayar ka sannan sai ka taba alamar Jirgi wanda yake kulle dukkan Network din wayar ka wato ( Airplane ) bayan ka kunna sai kaje inda kake dannan Numbobi idan zakayi kira sai ka Rubuta wannan code din (*#*#4636*#*# ) da zarar ka dannan Star ta qarshe zai bude ma wani zabin (optione ) aciki zakaga Phone Imformation to sai ka shiga ciki bayan ka shga zakaga ya nunoma wasu numbobi da rubutu sai kayi kasa a hankali zakaga MOBILE Radio Power zakaga Ma kunni a gaban shi sai kaje ka kunna to da zarar ka kunna shikenan ka kunna datar ka. " Amman shi wannan hanyar kawai zakakayi amfani da DATA ne batee da an kira ka ba ko ka kira ba ko kuma sako ya shigo har sai ka cire wannan Airplane din bayan ka gama amfani da DATAR.
2) Zakayi amfani da wasu Code wanda zai baka damar katse kiran waya amman zaka iya amfani da Datar wayar ka sannan zaka iya kiran mutum a wannan yanayi ko kuma a turoma da sako ko kuma kai ka tura kawai shi de wannan kirane bazai shigo ba .
Zakayi amfani da wasu code sune: ( **21*00000000#) amman ga masu amfani da layin 9mobile ko airtel wajen 0000000 zaku iya kirkirar Numba sai ku saka. kana dannan wajen kira shine zaka kashe kiran duk wanda zai kira ka. sannan idan layi biyu gareka sai ka dannawa kowannen su.
Sannan code din da ake cirewa Sune ( #21# ) da zarar ka saka wannan shkenn ka cire wannan tsarin da ka shiga
amman inde baka saka #21# ba to tabbas kira bazai taba shga wayar ka ba.
3) Application din da ake kashe datar duk wani abu da yake shan ye maka dan MB din sa ka saka a waya shine zakayi amfani da application ne saboda haka zai fada mana guda biyu sai kuje kuyi download din su
(a) V Guard
(b) Netguard
gaskiya na biyun yafi shine Netguard.
4) Hanyar da zaka cire duk wani tsarin kamfanin waya da ya saka ka yake debe ma kudi sune ga su zai zayyano
(a) MTN zaka dannan wannan code din (*123*5# ) bayan ka dannan zai kawo ma zabi (option ) sai ka zabi na uku zakaga unconfirm services sai ka zaba zasu baka zabin da zaka cire tsarin idan kuma baka cikin kowane tsari zasu fada ma.
(b) Airtel zaka tura sako ( STOPAUTORENEW zuwa 440 ).
(c) 9mobile zaka tura sako ( STOP zuwa 229)
(d) Glo zaka tura sako ( CANCEL zuwa 127).
Dukkan su da babban baqi za'a rubuta sannan a tura kamar yanda na Rubuta su.
#KKTechtube.