Yanda zaka dawo da duk wani hotunan da ka goge a wayar ka koda sunyi shekara


 Yanda zaka dawo da duk wani hotunan da ka goge a wayar ka koda sunyi shekara.

 Assalamu alaikum yan'uwa ina muku barka da wannan lokachi. Yau darasin mu akan wani application da kuka dade kuna jiran sa. Wanda zai baka damar dawo da duk wani hoto ko videon da ka rasa a wayar ka koda ya dade da goge shi wannan application zai taimaka ma ya dawo ma da su.

 Nasan da yawa mutane zasu ce kamar saboda su akayi wannan darasin saboda an dade ina yawan tambayana akan wannan hanyar musamman wani bawan Allah da ya rasa daya daga cikin password din sa wanda yayi screenshot ya ajje a wayar to daga baya yayiwa wayar tasa Format.

 Wannan application yana daya daga cikin sahihin application wanda aka yarda da su. Bayan haka akwai software ta computer mai irin wannan sunan wanda zai taimaka ma ka dawo da abinda ka goge na na kan computer ne ko kuma na kan memory ko flash din ka. Saboda haka koda ka mallaki application na waya ya kamata ka mallaki na computer ma. Akwai hanyoyin da na koya yanda zakayi download na software ta computer sai ka bi wannan hanyar sannan ka dakko ta. Wannan nayi muku bayani kan software ne.

  Zamu ahiga cikin darasin kai tsaye.

 Zan ajje muku link din application din a chn kasa sai kaje ka dakko shi ka ajje shi a wayar ka ko kuma ka ajje shi a duk inda kasan bazai bace ma ba.

 Bayan ka dakko wannan application yana da sauki wajen amfani da shi wanda batare da kasha wahala ba kawai zai nuna ma inda zakayi backup ma files din naka. Bayan ya gama zai fadama adadin abubuwam da suke acikin files din bayan nan zaka iya yi wannan restore din kamar sau biyu haka. To wani videon ma ko hoton ma ka manta da shi a wayar ka amman zaka ga ya dawo. Insha Allah.

 Tuntuni na yi videon wannan darasin a kan youtube dina mai suna KKTechtube saboda haka sai k ziyarchi youtube din sannan ka kalli videon domin karin bayani duk da de wannan application bashi da wani wahala wajen amfani da shi.

DOWNLOAD

DOWNLOAD

 Yanda zakayi download na wannan application achan kasan zakaga nace DOWNLOAD to kawai sai ka taba zai kaika inda zaka sauke wannan application akan wayar ka cikin sauki.


 

Post a Comment

Previous Post Next Post