Yanda ake tura message zuwa wata wayar a kyauta

 


Assalam barkanmu da wannan lokachi. Duba da abubuwan da suke faruwa na yawan chanja waya da muke tsinkar kanmu a ciki shi yasa yau nayi waiwaye akan wani application wanda zai bamu damar tura sakon da yake a tsohuwar wayar mu zuwa sabuwar wayar da muka chanja batare da ko guda daya mun rasa shi ba.

 Wannan application da na ke bayani akan sa yana da matuqar amfani da kuma matuqar sauki wajen amfani da shi a wayoyin mu. Bayan nan yana da amfanin da ya kamata mu mallake shi koda kuwa badan mu ba saboda yan'uwan mu ko abokan mu. Da zarar kana so ka chanja waya zaka iya tura dukkan sako message kenan  wanda kake dashi acikin adalin wayar ka zuwa sabuwar waya da ka chanja. Tuntuni na ajje muku link din wannan application a chan kasa sannan nayi bayanin wannan application kamar yanda na saba acikin video na a youtube kenan. Saboda haka sai kie chan ksa zakaga nace download sannan rubutun ya koma kore to da zarar ka taba shi shine zai baka damar sauke application din a wayar ka. Amman zan dan yi karin bayani akan application din saboda haka ka tsaya ka karanta rubutun gaba daya.

KARIN BAYANI.

 Wannan application bayan ka dakko shi a duka wayoyi guda biyun zaka saka da tsohuwar wayar ka da kuma sabuwar wayar taka. Sai ka bude application din a dukkanin wayoyin naka. Amman kafin nan dai ka hada wireless (wifi) kenan a tsakanim wayoyin naka. Shina a tsuhuwar wayar taka sai ka kunna hotspot sannan a sabuwar ka kunna wifi sai kayi connect. Bayan kayi connect ko ince da hausa hadawa sai ka shiga cikin application din a dukkanin wayoyin naka guda biyu. bayan ka bude to normal applicatiok din zai baka damar bude sabon applicatiom kamar yanda ka saba. Misali wajen allow da kuma confirm da dai sauran su. To bayan ya bude ma zakaga ya nunoma wasu rubutu guda biyu akwai (Send) sannan akwai (receive) to a tsohuwar wayar taka sai ka taba send ita kuma a sabuwar sai ka taba receive. To a tsohuwar da zarar ka taba send din zai nuno ma wasu lambobi Code kenan to ita kuma sabuwar wayar taka sai ka dannan Receive shine zai tambaye ka Hotspot a wani gefen kuma wifi to sai ka taba wifi din shine zai baka damar saka wadancan lambobi da ya nuno ma a tsohuwar wayar taka sai ka saka su a sabuwar wayar taka. Kana sakawa zai baka damar tura wannan sakonnin naka (message ) kenan zuwa sabuwar wayar taka.

 Wannan shine taqaitaccen bayani akan wannan applicatiom mai amfani.

YANDA ZAKAYI DOWNLOAD NA APP DIN.!

A kasa zakaga download da koren rubutu sai ka taba shine zai baka damar sauke application din a wayar ka. 

Nagode 

kada ku manta da share zuwa abokanku

DOWNLOAD

Previous Post Next Post