Wannan application mutane da yawa sun dakko shi a saboda hakan ne ma ya kamata kayi gaggawar dakko shi a wayar ka kafin na gama bayanin. Amman zan danyi mana tsokachi kadan akan application din.
Amfanin wannan application shine idan kana amfani da Nomal whatsapp to idan ka dakko wannan application zakana ganin duk lokachin da mutum ko abokin ka ya hau online ko ya sauka online sannan zai qididdige ma adadin mintunan da yayi da kuma Awowin da yayi tun daga na jiya har zuwa lokachin da ka shiga cikin application din.
Application ne gaba daya babu wani abin wahala a cikin sa sai de nayi bayanin wannan application acikin videon dana dora a Youtube channel dina saboda haka idan baka kalla ba kayi kokari kaje ka kalla amman zan ajje muku link din sa achan kasa sai ka garzaya domin dakko application din. Amman kafin nan zan danyi bayani akan yanda fuskar application din yake.
Bayan ka dakko application din zai baka damar ka dannan allow to bayan ka danna application din zai bude sannan zaka ganshi kamar empty to sai ka lura a sama bangaren hannun daman ka zaka ga wata alamar plus (+) sai ka taba. Zai nuno ma wani bangare wanda aciki zakaga jerin wusu rubutu na farko Telegram na biyu Whatsapp na Uku kuma VK.com to sai ka taba Whatsapp din. Bayan ka taba zai bude ma wani bangare na daban domin ka saka numbar da kake so ka dinga ganin lokachin da ya hau online ko ya sauka ko kuma sauran Analytics din sa. To sai kaje ka kwafo lambar mutumin a whatsapp din sa amman idan ka haddace to nomal zaka saka number a wajen. Amman kada ka manta da saka Code din kasar ka kafin a zuba number misali. Mu yan nigeria muna amfani da +234 sai number wayar duk da nasan sauran kasashe duka suna amfani da code din kasar tasu. To bayan ka saka number shine zai qara bude ma wani bangaren domin ka saka sunan mutumin ko abokin naka. kana sakawa zakaga wannan sunan da ka saka ya fito a farkon page din ka. To inde ka saka number daidai duk lokachin da ya hau online wannan application din zai sanar da kai ya hau online ko ya sauka. Sannan idan ka taba kan number da ka saka shine zai qara budema duk wasu bayanai na mutumin na adadin hawa online din sa da dai dauran su.
Zaka iya goge number bayan ka Ja sunan da ka saka zakaga akwai Rename da kuma Delete to idan ka taba delete zaka goge mutum ta wannan bangaren sannan zakaga wani makunni wanda idan ka kashe to koda mutum ya hau online baza kaji alamar ya hau ba. Sannan zaka saka adadin numbobin da kake so akan wannan application sai de wani lokachin shi application din zai ce maka sai ka sayi premium.
TA YA ZANYI DOWNLOAD DIN APPLICATION DIN.
a kasa zakaga na rubuta DOWNLOAD sannan zakaga rubutun kore to idan ka taba shine zai kaika inda zaka sauke application din.
Nagode
Tags:
Application for Android
Application for iphone
computer
facebook
free browsing
games
hacking
telegram
Tv
Videos
websites
whatsapp
wifi