yanda zaka saurari kowane gidan radio a duk inda yake ta cikin wayar ka batare da ka biya ko sisin ka ba

 


Assalamu alaikum yanuwana a muslunchi ina muku fatan alkhairi barkan mu ya kokari ya fama da rayuwa to Allah ya sauwake mana ya taimake mu baki daya ameen.

 Yau na kawo mana wani application mai matuqar abin mamaki da kuma muhimmanchi domin da yawa mutane koda a iya jihat da suke suna buqatar sauraron gidan radion da yake wani jahar domin sauraron wani labari ko wani shiri. To wannan application bama iya kasa ko jaha zai bak damar saurara ba zai baka damar sauraron duk wani gidan radion da yake a fadin duniyar nan sannan a duk inda kake. Tambayoyi sun yi yawa ga abokanam mu ko yan uwan mu domin suna buqatar suna jin labarin kasar da suke musamman ma yanda zakana ganin abubuwan da suke faruwa a kasar ka amman kuma kai baka da wata kafa ta jin wannan sahihin labarin. To wannan application zai taimaka ma ka saurari duk wani gidan radio da yake sannan a duk inda kake.

 Tuntuni na gabatar da videon darasi acikin youtube dina kuma na tabbata da yawa sun kalli videon sai buqatar sauke application din. Kaje chan kasa zaka ga rubutu da koren kala na rubuta download to shine link din da zaka sauke wannan application din. Amman kafin nan zan danyi karin bayanin application din saboda haka ka karanta duka rubutun saboda koda baka kalli videon ba to zai taimaka ma.

KARIN BAYANI AKAN APPLICATION.

 Application ne da zai baka damar sauraron duk wata kafa ta gidan radio a duk inda kake. Nasan kun fahimchi yanda aikin application din yake saboda haka zamu shiga cikin darasin kai tsaye.

 Da farko bayan ka dakko application din normal application din zai bude ba tare da wata wahal ba bayan ya bude kamar de yanda kake bude sabon application. Zai nuno ma asalin yanda fuskar application din yake sannan zai kawo ma current location misali a inda kake da kuma radion inda kake to zaka iya saurara normal. Amman yanda zaka kamo sauran gidajen radion da kake so ka kamo sai kasa hannun ka akan screen din wayar ka sai ka matsashi zakaga hoton duniya sun fito anan zaka juya hoton duniyar nan zuwa map din kasar da kake so ka kamo gidan radion ta. Bayan ka kamo sannan zakaga list ko jerin duk gidajen radion da suke wannan kasar ko jahar  sannan zaka iya saurara. Idan kuma ka kasa kamowa ta wannan hanyar akwai wajen SERCH a kasa zaka iya tabawa sai ka rubuta sunan garin da kake so ka kamo gidan radion su.

 Wannan dan taqaitaccen bayani ne akan application din. Kamar yanda nace muku nayi cikakken bayanin akan youtube dina zaka iya zuwa domin kallon darasin.

BANGA LINK DIN BA!?.

Kada ka damu kaje kasa kadan zakaga na rubuta download da babban baki sannan rubutun zakaganshi kore da zarar ka taba shi zai baka damar sauke wannan application din.

👇👇👇👇👇👇👇👇

DOWNLOAD

Previous Post Next Post