Assalamu alaikum barkan mu da wannan lokachi yanuwana a muslunchi ya ruwa ina fatan de kowa yana yin noma😀. Dan ni naje kauye na sami gona ta wadda zanyi noman shinkafa. Ba cika ku zanyi da surutu ba.
Darasin yau garabasa ce domin wani application na kawo muku wanda zai baki damar amfani da duk wata hanyar da ake biyan kudi a cikin wani application zakayi amfani da shi a kyauta. Mutane nasan zasuyi mamakin wannan darasi ko wani yace ma gaba daya bai gane me nake nufi ba. Ku biyoni a sannu zan fayyace muku komai domin kowa ya amfana da wannan garabasa. Dukda dai nayi cikakken videon darasin acikin youtube channel dina nasan da yawa mutane sun kalle shi to amman koda ace kai baka kalli videon ba idan kachi karo da wannan rubutun zai sauwake ma ka mallaki application din amman ina gayyatar ka da kaje kayi subscribe na channel din tawa mai suna kkTechtube a youtube channel.
Sannan sai kaje chan kasa zakaga link din application din domin ka sauke shi a kan wayar ka.
Akwai wasu lokutan zaka iya karo da wani application na kallo ko na yin game to da zarar zaka bude wani video zasu ce sai ka biya kudi wanda zaka saka atm na bankin ka sannan su ciri kudin ko kuma wata game wadda idan kana son shiga wani bangare ko siyan wani abu aciki sai ka biya su kudi to irin wadannan application na kawo mana wata hanya da zata baka damar amfani da dukkan abubuwan dake cikin wannan application din a kyauta. Bayan nan na kawo wannan darasi domin ilmantarwa badan ka cuci wani ba dan Allah mu kare hakkin mu da na mutane domin haduwa da Allah lafiya yan'uwa.
KARIN BAYANI
Wannan application din da zarar ka mallake shi acikin wayar ka kawai zaka budeshi da dukkan wasu abubuwa da kake buqata kamar allow ko comfirm kamar de yanda kake amfani da sabon application. To bayan ka bude shi zai fitoma da dukkan wani applications da yake a wayar ka sannan zai fadama duk wani application da abubuwan da yake amfani da shi. Misali. idan akwai talla acikin application din ko kuma ana biyan kudi aciki to zai fadama komai na application din. To sai ka zabi application din da zaka chanja kalar komai na cikin sa.
Link din application din yana chan kasa kaje sai ka sauke shi a kan wayar ka sannan ka bibiye mu a cikin youtube din mu domin ganin cikakken bayanin application din.
TAYA ZAN SAUKE APPLICATION DIN A WAYA TA?.
Zakaga koren rubutu na rubuta DOWNLOAD to sai ka taba zai kaika direct inda zaka sauke shi domin application din a website yake.