Assalamu alaikum ina muku fatan alkhairi.
Yan'uwa yau na kawo mana wani application mai matuqar amfani ga duk masu amfani da wayar android. Wannan application din zai baka damar amfani da wayar ka batare da kayi amfani da taba screen din wayar ta ka ba. Ta wani salo na daban wanda na gano wannan hanya a dan wannan lokachin.
A takaice de tuntuni na dora videon darasin a youtube channel mamu kaje kaga cikakken bayanin sannan kuma zan ajje muku link din wannan application din a chan kasa. Amman kafin nan zan danyi karin bayani akan application din a kasa.
KARIN BAYANI.
Wannan application mai suna Button mapper zai baka dama ne ka chanja duk wani salon da wayar ka take da shi domin gudun samin matsalar ta wani abu a wayar ko kuma saukakewa ga shiga wani bangare na wayar.
Misali da yawan gaske wani lokachin xakaga wayar ka wani bangare na screen din ya daina tabuwa ko kuma baki daya inda kake yin Back ko Home ko menemize to wannan application zai baka damar saita duk inda kake so ta amfani da volume din wayar ka sama ko kasa sannan idan ka tashi danna shi zakayi sau daya ko sau biyu ko zak dan danne shi ne ko de wani abu makamanchin hakan.
Hakazalika ba iya volume ba akwai abubuwa da yawa da wannan application yake da shi saboda haka batare da bata lokachi ba kaje kasa zakaga na rubuta download da babban baki to sai ka taba shi. Shine zai baka damar dakko application din sannan kayi amfani da shi.
Nagode