Daga yau an daina cutar ka idan kaje siyan waya.! Ga wani Application ||Darasi,Android



 Assalamu alaikum barkan mu da warhaka yan'uwa. 

Yau zanyi mana bayani ne kan wani application din da kuka dade kuna neman sa wanda bakowa yasan da shi ba. Sau dadama zakaga kanason zuwa kasuwa ka sayi waya wadda ba sabuwa ba ko kuma zaka siya wajen wani abokin ka ko dan'uwan ka to kana tsoron ko wannan wayar taba da wata matsala wadda ba lalle ka gane ta ba a lokachi daya. Wanda zakaga idan a kasuwa ne baya wuce kwana biyu zasu baka garantin wannan wayar. To amfanin wannan application shine zai binciko ma duk wata matsalar da take a waya ko wace kala ce hatta kara (Sound) ko karfin network ko abinda ya danganchi batteryn wayar. Koda wayar ka ma zaka iya gwada wannan hanyar domin gane duk wata matsala da take a wayar taka wadda kake so ka gano ta.

Tuntuni akwai cikakken videon darasin akan youtube dina zaka iya zuwa ka duba videon sannan insha Allah zan ajje muku link din videon.

Bayan nan akwai application din zan ajje muku link din sa achan kasa saboda haka sai kaje chan zakaga link din amman ka tsaya zan danyi bayani akan application din koda baka samu ka kalli videon ba.

Wannan application da nake ta zayyano bayanan sa yana dauke da abubuwa muhimmai kamar de yanda na fada muku a farkon rubutun nawa. 

Da farko de bayan ka bude wannan application din kamar yanda kake bude sabon application to zakaga wata alama ta kunnawa ko nace da turanchi play to da zarar ka taba ta shine zakayi scan na duk wata matsala da take a wayar taka sannan tana nuna ma alamar good idan abin bashi da matsala idan akwai matsala zakaga ta cancel din wannan abin alamar akwai matsala kenan.

 sannan acikin wannan applicationa akwai wasu hanyoyin da sai ka siye su. Amman baka da wata matsala idan ka siya din domin zai baka dukkan abinda kake so.

Yanda zakayi download din application din.

A kasa zakaga na rubuta download da babban rubutu sannan kuma rubutun ya zama kore. To da zarar ka taba shine zai baka damar sauke application din a wayar ka.

DOWNLOAD

Previous Post Next Post