Assalamu alaikum. Ina wunin mu yan'uwana musulmai ina muku barka da wannan lokachi a duk inda kuke. Darasin mu na yau shine na kawo muku wani application wanda zai baka damar kulle iya wani chatting na mutum. Misali budurwar ka, saurayinki, abokin ka, ko kawarki ko kuma wani group wanda kika ko ka kebe. Nomal munsan idan zaka sakawa whatsapp din ki password dole sai de ka sami wani application ko kuma wanda wayaak zuwa da shi wanda gaba daya whatsapp din kake kullewa. To shi wannan application yasha banban da irin wadannan application. Domin kawai zai baka damar kulle iya wani chatting na mutum daya ko daidaiku wanda ka ware tare da group idan kana buqata. Zaka iya barin whatsapp din naka babu password ko wani security amman da zarar za'a bude ma wani chatting wanda ka kebe dole sai an saka password din da ka zaba wanda ka kulle wannan chatting din. Yanda da amfani ku mallake shi.
Tuntuni na dora videon shi a kan youtube channel dina sai kaje ka kalla sannan na ajje muku link din wannan application achan kasa domin kowa ya mallaka. Amman kafin nan yakamata ka tsaya ka karanta rubutun gaba daya domin zan dan qarayin bayani akan shi wannan application din.
KARIN BAYANI!
Application ne da zai baka damar kulle iya wani chatting wanda ka kebanche kake buqatar ba wanda zai shiga sai ya saka security aciki. Kamar de yanda nayi muku bayanin sa a farkon rubutun.
Da farko bayan ka dakko application din noaml zaka bude application kamar yanda kake bude sabon application amman a karshe zai kawoma wajen inda zaka saka password. Shi kuma a wajen idan ka lura da dan rubutun saman zakaga yanda bayani akan cewa ka kirkiri password mai dauke da numbobi guda hudu bayan ka saka kuma ka dannan next zai qara kawo ma domin ka qara maimaita wannan numbobi guda hudun wanda ka fara sakawa bayan ka sa su to shine application din zai bude ma gaba daya!.
Idan ya bude ma gaba daya zai baka damar saka gmail dinka a wajen domin koda ka manta wannan password din na ka wanda ka saka tsaro acikin whatsapp din ka idan kana so sai ka taba Enable idan baka so sai ka taba skip. Amman shawara ya kamata ka taba Enable din domin ka saka gmail din naka saboda gudum samun matsala. Kana taba Enable shine zai kawo ma gurin da zaka saka wannan gmail din naka bayan ka saka zakaga save sai ka taba. Shikenan ka bude wannan application din.
Bayan gaba daya application din ya bude a kasa zaka lura da dan rubutu guda biyu akwai direct whatsapp sannan akwai add user. Afwa ba lalle wannan rubutun suka rubuta ba amman tabbas akwai rubutu guda biyu. To sai ka taba na farko hannun ka na hagu kennan daga kasa. Bayan ka taba direct zai kaika whatsapp din naka bayan ya kaika shine zaka zabi sunan wanda kake so ka saka masa security to anan zaka zabi iya adadin wanda kake so ka saka daya bayan daya kenan. Harda group din naka da kake so ka sakawa.
Kana bin wannan hanya shikenan ka kulle sannan zakaga duk user din da ka saba acikin wannan application. Sannan a gefe zakaga alamar Kwado (key).
YANDA ZAKAYI DOWNLOAD DIN APPLICATION DIN.
A kasa zakaga na rubuta download da babban baqi sannan zakaga ya zama kore to sai ka taba shine zai kaika asalin inda zaka sauke wannan application din