Assalamu alaikum barkanmu da warhaka ya damina. Ina fatan kun yi noma kamar yanda nima nayi😀. Dan babbar gona na samu na noma saboda tsaro hhhh.
Darasin mu na yau zanyi bayani akan wani boyayyen application wanda ya kamata ku mallake shi domin zai taimake ku bangaren dukkan wani sassa na wayar ku.
Zakayi amfani da screen din wayar ka batare da kayi amfani da button din wayar ba.
Akwai lokutan da zaka iya wayar gari button din wayar ka ya daina amfani ko nace ya daina dannuwa. To shi wannan application zai taimaka ma batare da kayi amfani da button din ba zakayi amfani da wayar ka da zarar ka rubuta kalmar da ka saita da ita.
Tuntuni na dora videon darasin akan youtube dina sai ka ziyarche shi domin kallon cikakken darasin sannan kuma na akje muku link din application din achan kasa. Sai kaje ka dakko shi domin ka saka shi a wayar ka.
Wannan application bashi da wahala wajen amfani da shi ko wajen bude shi.
Yanda zakayi download din application din.
Zakaje chan kasa zakaga na rubuta download da babban baki sannan da koren rubutu sai ka taba shine zaka sauke application din a wayar ka.