Yanda zaka gane ana bibiyar wayar ka


 Assalamu alaikum ina muku barka da wannan lokachi. A gurguje wani application ne mai matuqar amfani wanda ya kamata mun mallake shi domin zai binciko mana duk wani boyeyyen application da aka boye shi a wayar mu yana daukar bayanan mu.

 Sau da yawa nakanyi bayani akan irin wadannan abubuwan domin gujewa afkawa irin wannan hali. Akwai lokachin da kai baka sani ba za'a iya saka maka wani application domin ya dauki wani bayanan ka baka sani ba. Sannan za'a iya boye maka shi acikin wayar bazaka taba ganin wannan application din acikin menu dinka ba. To yau shi yasa na kawo mana wani application da zai binciko mana duk wani application da zai iya bawa wayar mu matsala. Da kuma aka boye shi bamu san da shi ba .

Sannan zai rarrabe mana banbanchin System application da kuma user application domin gujewa wayar mu kada ta sami matsala.

 Tuntuni shi dai wannan darasi na rigada na dorashi akan youtube dina ga duk mai son yaga cikkaken videon darasin zai iya ziyartar channel din tawa. Sannan shi application din kaje chan kasa  zakaga link din sa sai kayi download din sa. Amman kafin nan ya kamata ka tsaya ka dan karanta bayanin da zanyi akan shi wannan application din koda baka ga videon darasin ba wannan zai taimaka ma sosai.

 KARIN BAYANI.!

 Applucation ne da bashi da wuyar amfani batare da kasha wuya ba zai rarrabe ma duk abubuwan da na fada a farkon darasin. Da zarar ka sauke application din a wayar ka kawai sai ka bude shi. Bayan ka bude shi shine duka zai jero ma abubuwa.

To anan zamuyi maganar Hidding app ne. Misali application da yake a boye baka ganin sa to a farkon jerin ma shi zaka fara gani.

Da zarar ka shiga zakaga duk wani application da aka boye ko ya buya a wayar ka ko guda nawa ne. Idan kuma babu zakaga wajen babu komai to shine babu wani application da ake bibiyar ka.

TAYA ZAN YI DOWNLOAD NA APPLICATION DIN?

A kasa zakaga na rubuta download rubutun zai ksance kore sannan zakganshi babba to sai ka taba shine zaka sauke shi a wayar ka!.


DOWNLOAD

Previous Post Next Post