Application guda biyu masu abin mamaki ga masu amfani da wayar Android 2022

 


Assalamu alaikum barkan mu da warhaka yan'uwa ina muku fatan alkhairi yau darasin mu na kawo mana wasu applications guda biyu masu abin mamaki da kuma amfani sosai.

Kowanne daya daga cikin su yana da amfani maquta domin kuwa zai baka kariya ne daga daukar duk wata hanya da ake daukar bayanan ka.

 Application na farko zai bayyano ma duk wata kafa da ake daukar bayanan ka kamar daukar hoto ko video.

 Akwai application da yawa da suke amfani a background din wayar ka suna daukar video ko hoto ta camerar gaban wayar ka baka sani ba.

To da taimakon wannan application din zaka iya binciko wane application ne yake dakko maka ko yake daukar videon naka. tuntuni na dora videon wannan darasi akan youtube dina zaka iya zuwa ka kalli cikakken videon akan dukkan darasin.

Application na biyu zai baka damar sauke duk wani application da kake dashi akan wayar ka wanda zai sauka akan memoryn wayar taka. Wanda koda ace kayi rashin application din zaka iya dawowa dashi batare da ka sake dakko wani ba.

 Da zarar ka mallaki application din  bayan ka shiga cikin sa zai fito ma da duk wani applications da yake a wayar ka.

To sai ka zabi application din da kake so ka ajje da zarar ka taba shi batare da yaja wani lokachi ba zai sauka akan wayar taka.

Dukkan wadannan application suna da matuqar amfani gare mu masu amfani da wayar android yau da gobe. Ya kamata mu mallaki wannan application masu amfani.

Zan ajje muku link din application din achan kasa zakuga nace Download da ka taba shi shine zai kai kaninda zaka dakko kowane application na daya da na biyu.


DOWNLOAD 1

DOWNLOAD 2

Previous Post Next Post