Remote// Yanda zakayi amfani da wayar ka a matsayin remote din tv ko AC sabuwar fasaha 2022



Assalamu Alaikum barkan mu da warhaka ya ruwa Allah ya bamu mai amfani. Yau kam anyi ruwa sosai tun safe har wajen sallar azhar hakan yasa ma bansamu na fita kasuwa ba.

Ganin wannan yanayin ne yasa na binciko mana wani application wanda da yawan mu muna buqatar sanin wannan fasahar. Zakayi amfani da wayar ka ta hannu domin hada (Connect) duk wata device da kake so kayi control a matsayin remote batare da ka ta bata kudin ka wajen siyan battery na Nomal remote din ka ba.

Idan kuka biyo mu a sannu a hankali abin babu wata wahala zakayi amfani da wayar ka a matsayin remote a kowane yanayi kake sannan kuma a kowace kalar waya iphone ko android. Duk da dai na rigada na dora videon darasin akan youtube dina ga duk masu buqatar ganin cikakken darasin sai su tafi youtube dina mai suna KkTechtube domin kallon darasin acikin cideon. Sannan kuma ga duk wadanda suke buqatar mallakar wannan application sai suje chan kasa na ajje link din sa domin amfani da shi.

Acikin videon ma farayin bayanin yanda zaka saita na wayar iphone daga baya na nuna na wayar android.

Idan kana amfani da wayar iphone farko inda zakaga remote din nata ka shiga cikin setting din kan wayar ka bayan ka shiga sai ka nemo Conrol center acikin nan zakaga Apple tv remove to zakayi la'akari a bayan rubutun wace alama ce idan alamar minus (-) ce to ba sai ka qara tabawa ba kawai da zarar k janyo inda kake kunna datar wayar ka zakaga remote din ya fito. Amman idan alamar plus (+) ka gani sai ka taba alamar shine zai baka damar sauke shi a wajen inda kke kunna datar wayar ka. Daga nan idan ka bude remote din shine zakaga yana searching amman ka tabbafa da kaje kusa da abinda kake so ka saita da shi AC din ko TV din shine zai kama sunan wannan device din.


 Masu amfani da android kuma ga link nan a kasa na ajje muku sai kuje ku sauke shi. Babu wahala wajen hada duk abinda kake so kayi control da shi. kamar. Receiver,AC,TV da sauran su. 

Sannan duk masu amfani da iphone idan waccan hanyar batayi ba zaka iya shiga appstore ka dakko application mai suna Universal Remote control. Zai yi duk abinda kuke buqata.

 YANDA ZAKA DAKKO APPLICATION DIN.

A kasa zakaga nace download sai ka taba shine zai baka damar sauke wannan application din a wayar ka.

👇👇👇👇👇👇👇

 DOWNLOAD

Previous Post Next Post