An chanja ma Imei din wayar ka baka sani ba😭

 

Assalamu alaikum yan'uwa barkan mu da sake saduwa a sabon darasin mu na yau. Yau zamuyi darasi ne akan yanda zaka gane idan wayar da ka siya ko zaka siya ko an chanja mata imei na wayar. 


MENE NE IMEI.


Wasu numbobi ne wanda suke zuwa a kowace waya haka zalika kowace waya tana da nata imei din bayan nan ta wannan imei din koda wayar ka ta bata za'a iya gano inda take wati (Location ) kenan. 

Sannan dukkan wadanda zuka san sirrikan kutse na waya zasu iya yi maka kutse ta amfani da imei naka hakan yake sawa ya kamata ka mayar da abin sirri ba kowa zai san da shi ba.


Sannan lambobin da zaka iya gano wannan imei din wayar taka ka shine. A kowace waya a jikin kwalin ta akwai wannan imei da kuma bayan wayar da cikin wayar wajen setting. To amman idan duka guraren nan baka da su ko zasu baka waya akwai wani code wanda zai baka damar fito ma da imei din wayar zaka dannan *#06# kana dannawa zaka wannan imei din ya fito na wayar ka.


 TO ME YASA AKE CHANJA IMEI DIN BAKA SANI BA? KUMA MENENE RIBAR YIN HAKAN?


Ana chanja imei ba waya ne domin chanja dukkan wasu abubuwa da ta zo da shi da kuma badda kamanni. Duka zan amsa wannan tambayar a dunkule. Na farko idan wayar sata ce ko aka tsinta sannan ba'a so ayi tracking din wayar domin a siyar da ita. Za'a iya chanja mata imei yanda babu wata hanya da za'a iya gano inda take. ko kuma an ciwo wani bashin kamfani za'a iya chanja mata imei number.


TO AKWAI MATSALA KENAN?.


Ba qaramar matsala ba saboda idan aka chanja mata imei a fitar da ita daga da'irar asalin kamfanin ta. Hakan yake sawa zakaga wasu wayoyin idan an chanja imei da zarar ka kunna su zasu fada maka akan cewa basu da alhakin wannan wayar domin akwai matsala akan ta saboda chanja imei din da akayi. Bayan nan babban matsalar shine da zarar kayi mata restore ko wipe din wayar to Network zai sauka bazai hau ba sai de idan ka qara biyan kudi sannan a qara chanja ma imei dinta. Ya kamata a kula sosai.


TA YA ZAN GANE AN CHANJA MATA IMEI DIN TO?.

Hanya ce mai sauki, da zarar ka dannan wadannan code din *#06# ko kuma ka gan imei din kamar yanda nayi muku baynin yanda ake ganin su sai ka copy din su. bayan nan sai kaje wannan website din ga link din sa nan a kasa sai kayi paste din imei din to zasu fada maka komai akan waya koda an chanja.

Ga link din website din

👇👇👇👇👇👇👇

IMEI



Previous Post Next Post