Yafi kowane application na wayar Android kowace kala ce amfani 2022



Assalamu alaikum ina muku fatan alkhairi. Yau darasin mu zanyi bayani ne akan wani app wanda tuntuni nayi muku bayanin sa acikin videos sai de saboda yawa mutane suna ziyartar wannan kafa tamu domin samin wasu application masu matuqar amfani.

 Application din zai baka dama copy din wata kafa da kowane website ko text din da computer ko device bai baka damar copy ba. Sai de nasan wasu zasu ce na shigar da su duhu. Domin sunji wani kalar bayani to kuyi hakuri zanyi kokarin fahimtar da ku insha Allah.

 Akwai abubuwan da kowane kalar application ko website wanda babu su acikin lissafi. KAMAR. Screenshot akwai app ko website wanda basa bayar da damar kayi screebshot na wannan manhaja kamar app na bank ko na wani babban kamfani ko na makaranta ciki harda irin website da akeyin kwallo kamar irin su Netflix. babu damar kayi screenshot aciki sai de idan ka samu wasu yan dabaru sannan kayi.

To wannan ma amfanin sa shine idan kana so kayi copy na rubutu kamar  idan ka shiga wani website zakaga basa ba da damar kayi copy na wani rubutu aciki dole sai de ka karanta ka fita. 

Shi wannan application zai baka damar copy din dukkan abinda kake so kayi amfani da shi. Koda ma ba iya website din ba harda inda kwata-kwata ba'ayin copy kamar screen din wayar ka.

Sannan bayan ka copy wannan rubutu zaka iya fassara shi zuwa kowane kalar yare.

 Nasan duk kun kalli wannan cikakken bayanin da na dora a facebook.

Saboda haka zan ajje muku link din app din a kasa zakaga nace Download sai ka taba shine zai baka damar dakko wannan app mai mihimmanchi.

 Ga link din sa nan a kasa

👇👇👇👇👇👇

DOWNLOAD

Previous Post Next Post