A karshe de yanda zakayi Tracking ka kama barawon waya da hoton sa da garin su

 Assalamu alaikum bayan sallama irin ta Addinin muslunchi. Zan qara da Alhamdulillah dukkanin jiran da kukeyi yazo karshe domin wasu application guda biyu na kawo muku domin yin track na wayoyin ku batare da wani bata lokachi ba. Dukde da na tabbata kun kalli dukkanin cikakken video a facebook page dina mai suna KK Techtube amman zan danyi qarin bayani akan application din duka guda biyu. Saboda wata qila ba kowa bane ya kalli videon.

Wadannan application suna da matuqar amfani ga wayoyin mu domin da zarar ka saita su zasu baka damar gane asalin barawon wayar ka hoton sa da garin su da inda yake. Koda ashe ma ba sace ma wayar taka akayi ba. Zaka ita bin diddigin ta ka gano inda ta fadi.

 Rashin waya ya kasu kala daban-daban akwai wanda wayar faduwa take wani ma baisan a inda ta fadi ba hakan yake sawa mutum zaice an sace masa ita.

Akwai wanda kuma daukewa mutum ake cikin ajjihu ko jaka. Ko ya saka chaji a wani gurin.

Wani akan ita zare masa makami domin a tsoratashi ko ama yanke shi domin ya bada wayar tashi.

Wani kuma chin amana ne may be abokin sa ne a cikin daki zai dauki wayar tashi. Amman saboda yanda suke da juna babu damar a chaje shi. 

Bayan wannan ma zaka iya ajje wayar taka dan ka ko matar ka suyu kokarin bude ma securityn wayar taka.

To koma de menene batan waya yana da zafi sosai. Sannan wadannan application zasu taimaka ma inde kabi dukkanin hanyar da na koya a cikin videon. Sannan ga wadanda basu ga videon ba zan ajje muku shi a kasa domin ganin cikakken yanda ake amfani da su baki daya.

Saboda haka ga videon nan kawai taba zakayi zai bude sannan sau kaga yanda ake saitawa.

👇👇👇👇👇



To Zan danyi bayani akan application na farko wanda na farayin bayanin sa acikin videon. 

Bayan nan dukka wadannan application din zaka fara saita su ne kafin wayar taka ta fadi ko a sace. 

Sannan wannan track din ana amfani da Gmail ne bada IMEI ba. Sannan nayi wannan videon ne badan komai ba sai dan ilmi. 

Amman da zarar kun tabbatar da wayar taki an sace ne sai ku garzaya police station domin su bincika ma Nagode.

Shi wannan application din wanda zan ajje muku link din sa a kasa bayan ka sak shi acikin wayar taka. Zai baka damar saka gmail din ka bayan ka saka gmail din ka akwai saita-saitan da dole sai ka kalli videon sannan zaka san yanda zaka amfani da shi. 

Amfanin sa shine. Da zarar anyi  kokarin cire securityn wayar ka to wayar ka zata dauki hoton barawon. Ya turoma ta cikin gmail din ka. sannan ta cikin hoton zaka iyayin track har inda barawon yake. Kamar de yanda nayi muku bayani acikin videon.  Sabo da haka yana da amfani sosai ganin videon.

Application na biyu kuma na karshe. Shina zai baka damar gane asalin wanda ya dauke ma wayar ka. Sannan shi wannan application babu wahalar saitawa ba kamar na farko ba. Da zarar ka saka gmail din ka zai baka damar daukar dukkanin hoton wanda yayi kokarin budema security koda kaine idan ka saka ba daidai ba. Sannan shi wannan application na karshe zai baka damar kunna wayar ka tayi qari koda ace an kashe wayar taka. Amfanin qarar shine . Idan kuna zargin a inda kuke barawon yake to kafin kowa ya bar wajen zaku iya amfani da wannan kusa wayar tayi qara sosai. Da dai sauran abubuwan da kuka gani acikin videon.

YANDA AKE TRACK DIN

Da zarar wayar an sace ta sai k Ari wata wayar sai ka dakko irin wannan application din duka guda biyun inde ka saita da gmail din ka. To sai ka sa gmail din naka. Kana sakawa ta nan zakaga hotunan barawon to ta wayar wanda ka Ara din zakayi tracking din ta.

Amman kallon videon lalle yana da amfani.

Ga link din application din na farko dana biyu. Idan kaga an rubuta (Download 1) To application na farko kenan. Idan kuma kaga an rubuta ( Download 2) application na biyun kenan.

Amman da zarar ka tabbatar da wayar taka bata tayi sai ka garzaya police station domin cikakken bayani Nagode.

👇👇👇👇👇👇

DOWNLOAD 1

DOWNLOAD 2

Previous Post Next Post