application na Hada aure na sheikh Aminu ibrahim Daurawa

 


Assalamu alaikum barkan mu da sake saduwa a sabon darasin namu.

Duba da yanda wannan application yayi yawo sosai da kuma amfani yasa na kawo muku shi. Domin Application ne wanda ya danganchi aure.

Wannan application na Malamin mu Sheikh Aminu ibrahim Daurawa yayi shine domin duba da yanda ake ta yawan korafi akan maslahar aure.

Zan dayyi muku takaitaccen bayani akan wannan manhaja mai matuqar amfani. 

Da zarar ka mallaki wannan application acikin sa akwai ajujuwa gida uku (3) . Wanda malam yakeyin video lokachi bayan lokachi. 

Aji na Farko Malam ya tattauna akan dukkanin mutanen da suke neman aure Saurayi ne ko budurwa ko bazawara ko bazawari ko kuma iyaye suna sun nemawa yayan su mazajen aure ko matayen aure to gaba daya malam ya tattauna acikin videon ta yanda kowa zai bi domin samin ta gari. Da sauran shawarwari.

Aji na biyu malam ya tattauna acikin video kan wadanda sukayi auren sannan suna cikin zaman lpy to akwai irin shawarwarin da malam ya bawa irin wadannan ma'aurata domin jindadin zaman auren su da kuma me ya kamata su dage da yi acikin zamantakewar su.

Aji na uku malam ya tattauna ne akan ma'auratan da suke samin matsalolin zaman su. Misali suna da matsala a tsakanin su ko a tsakanin iyayen daya daga cikin bangarorin su. abinda ya danganchi family na miji ko na mata ko abokai ko qawaye ko kuma kuntatawa juna. To malam yayi cikakken video da kuma bayanai akan dukkanin ire-iren wannan matsalolin. 

Ya kamata ku mallaki wannan application domin qara jindadin auren ku.

Sannan shi wannan application gaba daya bashi da wani Nauyi kuma babu wani bagare na talla. Sannan lokachi bayan lokachi ake saka video a kowane bangarori. 

Akwai yanda zaku iya tattaunawa da malam kai tsaye. 

kuma wannan kamfani mai girma shi ya kirkiri wannan application wato KK Techtube.

Ga link din application din nan a kasa zaka ga an rubuta DOWNLOAD da zarar ka taba shine zai baka damar sauke app din a wayar ka/ki.


👇👇👇👇👇👇👇👇

DOWNLOAD

DOWNLOAD

Previous Post Next Post