Yanda zaka duba komai na BVN din ka batare da kaje banki b




 Assalamu alaikun barkan mu da sake saduwa a sabon darasin mu. Yau ma yan'uwa wani boyayyen abu na kawo mana wanda da yawa ana  buqatar sa akan BVN. Da yawa suna da BVN sannan suna so su san dame-dame suka rubuta ko wannan BVN din me yake dauke da shi. Misali Suna ko Date of birth da dai sauran su. Duk da wasu ma gaba daya basu san BVN din nasu ba. Gaba daya zan dan kokarta na yi bayani a takaice da kuma yanda zaka ga bayanan BVN din ka.

Farko de shi BVN dukkan wanda yake da Account a banki yana da shi. Sai de wani ma koda wadannan Lambobi guda 11 nan bashi da su. Saboda ya dauka kawai da zarar an bude masa BVN sannan an bude masa banki to bashi da wata matsala yasan da lambobin.

To a gaskiya ba haka bane ya kamata yanda kake adana dukkan abubuwan ka masu muhimmanchi to shima ka ajje shi koda a gida ne. ko kuma acikin wayar ka duk dai da akan sami matsala idan kayi save akan wayar ka bayan wayar ta fadi ko an sace.

Duk wanda ya bude BVN tunda akwai wanda suke fara bude BVN kafin su bude Banki. To dole sai an rubuta masa a takarda an basa ya ajje. Kuma koda a banki ne sai sun baka sun ce ka ajje shi a wajen ka. Amman idan akayi rashin dace takardar ta fadi zaka iya dubawa acikin layin da aka saka number waya wajen bude.

Idan zaka duba ta cikin wayar ka shine zaka dannan wadannan code din bayan nan za'a dauki kudi Naira 50 ko kasa da haka Code din sune 👉👉👉 *565*0#  Sannan kowane layi kake da shi wadannan code zaka rubuta zai baka wannan nambobi ma BVN din ka guda 11 sai ka ajje su.

To kuma idan kana da nambobin sannan kana so kasan komai akan BVN din naka misali. Wane suna ka saka ko wane Date ka saka da sauran bayanai na bvn din. Shimaa akwai hanyar da zaka iya dubawa ta amfani da wani website wanda zan rubuta muku kawai dannanwa zakayi zai budema sai ka saka wannan Nambobi naka ma BVN.

Amman zanyi muku bayanin yanda zaka duba idan website din ya bude ma.

Farko de ga website din👉👉 BVN CHECK Ga shinan a baya zaka ganshi da koren rubutu kana tabawa zai bude ma.

Ga bayanan da suke buqata.

Na farko dole sai kana da ATM card wajen biyan kudin da zasu baka damar dubawa. 

bayan website din ya bude zai ce ka saka Nambobin nan na bvn din anan zaka dannan Search bayan ya bude ma shine zai baka dama ka zuba Lambobin jikin ATM din ka domin su dauki NG25 bayan nan zasu baka damar bude duk bayanan BVN din ka.

GARGADI.

Wannan gargadi ne daga gareni ku lura da BVN din ku yana da matuqar hadari idan wani ya mallakeshi.🥲

Kada ku manta da share din rubutun nagode.

Previous Post Next Post