Yanda zakayi browsing a boye ( Private ) Domin boye sirrin ka 2022

 

Assalamu alaikum barkan mu da sake saduwa da ku a daidai wannan lokachi. Ya dan sanyi-sanyi.

Yau ma de kamar kullum wani website na kawo muku mai matuqar amfani da kuma sirri. Buguda qari wani ilmi ne da ya kamata ka tsaya ka nutsu kuma ka karanta gaba daya domin gane yanda abin yake. 
Asalin dukkanin abubuwan da mukeyi a wayoyin mu akwai sirrin da idan ba fada maka akayi ba baza ka fahimche su ba koda kuwa kana amfani da abin kullum!.

Ga cikakken videon website din ka danna kan hoton zai budema
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇



Zan danyi muku bayani akan internet da kuma muhimmanchin wannan website da na kawo muku.

Da zarar ka kunna Datar wayar ka kuma ka nemi wani application ko website domin ganin abinda ke cikin sa to shi wannan website ko application ya kan iya gane asalin wanene kai. Misali Garin ka ( Location ) da sauran su ip address din wayar ka da wane kalar layi kake amfani da dai wasu sirrin da baka sam da su ba sabo da baka da ilmi akan abin. Amman komar Datar ka yana sane da ita.

To kuma hakan yake sakawa ga masu wayo suna amfani da VPN wanda sukan chanja wasu abubuwa na wayar su domin boyewa ga wani application ko website wanda bazai gane asalin su wanene ba. Idan kayi amfani da VPN App ko software to fa zaka iya shiga website ko application bazai gane daga wane gari kake ba da kuma ip address din ka da duk wasu abubuwa da na lissafo a baya wanda akan iya gani idan ka ziyarchi wani website ko application.

 To shi kuma wannan website da na kawo muku yafi VPN amfani. Saboda shima zai baka damar shiga duk inda kake so to duk inda ka shiga bazai gane asalin daga ina kake ba ko ya dauki wani bayanai na wayar ka ba.
Amman idan kayi amfani da VPN dole ne sai ka saka wani application a wayar ka ko kuma Software a Computer ka. Domin amfani da VPN din sannan shi VPN akwai wanda yakan jawo maka matsala gaba daya. a wayar ka ko kuma yace sai ka biya kudi sannan zaka iya amfani da shi.

Amman shi wannan website zakayi amfani da shi batare da ka biya kudi ko kuma kana tsoron ya baka wata matsala a wayar ka ba. Hakan yasa na zabo muku wannan website ga dukkanin wanda suke son ziyartar wani shafi domin basa so a gane suwaye su.

 Idan zaka amfani da wannan website to koda an kulle site din ko application din ko chatting din a kasar ku ko a garin ku ko a wayar ka to wannan website zai baka damar ziyartar wannan site ko chatting.

Dan karami  misali👇👇👇👇

A dan shekarun bayane aka kulle Twitter ta daina amfani a nan kasar nigeria. Kwata-kwata koda ka shiga wannan application na twitter baizai yi ba saboda an kulle shi a nan nigeria. 

To da ace har yanzu wannan twitter a kulle take da zarar ka ziyarchi wannan website da zan baku zaka iya amfani da ita batare da wani matsalar network ko service ba.

Saboda haka gaskiya wannan website yana da amfani sosai.

Ga sunan sa nan a kasa. Sai ka nome browser Chrome ko Operar ko Safari ko duk wata browser da kake buqatar ka bude da ita. Sai ka rubuta abin da na ajje muku to zai bude.

👉👉👉👉 PROXYIUM.CON

Previous Post Next Post