Abubuwa 4 Da zaka kula da su Don Tsars Bankin Ka daga Masu Kutse ( Yahooboys)



Abubuwa 4 Da Zaka Kula Da Su Don Tsare Bankin Ka Daga Masu Kutse


Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Yau cikin yardar Allah zamu yi muku bayanin abubuwa 4 daga cikin abubuwan da mutum zai bi don tsare bankinsa daga masu kutse da suke kwashe kuÉ—in mutane a bankuna.


Bayan addu'a da mutum zai yi don neman tsarin Allah daga waɗannan mutane, dole kuma mutum sai ya yi riƙo da sababi, riƙo da sababin shine mutum yayi duk wani abu da zai iya yi wajen tsare bankinsa, wanda a ƙarƙashin wannan shine zamu yi muku bayanin abubuwa guda 5 da mutum zai kula da su don tsare bankin nasa:


1. Kula da Sim Card:- Dole mutum ya kula da Layin da ya buɗe account da shi, domin kuwa an tabbatar da cewa da Layin waya shi kaɗai ana iya kwashewa mutum kuɗinsa da suke bankinsa matuƙar Layin yaje wajen waɗanda suka iya yanda ake kwashewa ɗin, a ƙarƙashin wannan dole mutum ya riƙa taka tsan-tsan wajen bawa mutane wayarsa, ko kuma aje wayar tasa inda wani zai iya ɗauka, don haka a kula sosai.


2. Kula Da Bvn:- Ya zama wajibi mutum ya riƙa taka tsan-tsan da Bvn ɗinsa, domin shima an tabbatar da cewa ana amfani da shi wajen samun bayanai na mutum sai ayi amfani da waɗannan bayanan da aka samu ta dalilin Bvn ɗin nasa har ta kai ga an kwashe masa kuɗi a Bankinsa, a ƙarƙashin wannan yana da kyau a guji bawa mutane Bvn da sunan zasu cike maka wani tallafi da ake bayarwa, sannan a guji aje Bvn akan waya, haka kuma idan aka rubuta a takarda don a ajiye to a guji aje takardar inda wani zai iya ganinta, a guji buɗe bankunan online da ba a san ingancin su ba ko kuma waɗanda basu da license da babban bankin ƙasa, sannan a guji website da apps da suke bada bashin kuɗi, a kula sosai game da Bvn.


3. Kula da Atm Card:- Dole ne mutum ya kula da Atm Card ɗin sa, domin shima Atm Card an tabbatar da za a iya amfani da waɗannan nambobin da suke rubuce a jikinsa a kwashe kuɗin mutum da suke Bankinsa, don haka ya zama wajibi mutum ya riƙa taka tsan-tsan wajen bawa kowa Atm Card ɗin sa, musamman idan mutum zai yi aike a ciro masa kuɗi ya kamata ya san wanda ya kamata ya bawa, haka kuma ya kamata mutum ya riƙa saka ido idan yaje cire kuɗi a wajen masu Pos, sannan a rage yawan yawo da Atm Card idan ba amfani mutum zai yi da shi ba, idan kuma dole sai mutum yayi yawo da shi to ya riƙa kula sosai saboda kar ya jefar da shi, don haka a kula sosai.


4. A kula da danna Links:- Mutane ya kamata su riÆ™a kula da danna Links É—in da ake turo musu, sabo da akwai Links É—in da suke na cutarwa ne an Æ™irÆ™ire su ne don a cuci mutane, wani Link É—in dazarar mutum ya danna shi shikenan za a iya cutar da shi sanadiyar danna wannan Link É—in da yayi, wani kuma Link É—in bayan mutum ya danna shi  to duk bayanan da zai rubuta a wannan shafin zasu tafi ne wajen wanda ya Æ™irÆ™iri wannan Link É—in, shi kuma zai yi amfani da wannan bayanan yayi cutar da su, don haka a Æ™arÆ™ashin wannan mutane su kiyayi danna irin waÉ—annan Links É—in kamar haka:


- Duk Link É—in da ya fara da http ba https ba, a guji danna shi ballanta har mutum ya saka bayanan sa a ciki, link É—in da ya fara da http to shafin ba shi da tsaro.

- A guji danna irin waɗannan Links ɗin na samun kuɗi kyauta, ko kuma samun data ko katin waya kyauta, ko dai wasu abubuwan da sunan kyauta (free), a guje su ayi taka tsan-tsan da su, koda sun fara da https, saboda za a iya samun Link ɗin da ya fara da https kuma Link ne na cuta, a dunƙule dai duk Link ɗin da ya fara da http kar a danna shi, idan kuma ya fara da https to a tsaya a tabbatar da ingancinsa kafin a danna shi har a saka bayanai a ciki, don haka ayi taka tsan-tsan matuƙa game da Links.


Allah ubangiji ya tsare mu baki É—aya

Previous Post Next Post