Hanyoyin da akeyin hackin da satar bayan mutane 😭 ( A kula sosai )



Ka kula da irin applications ɗin da zaka riƙa saukewa akan wayarka da kuma irin website ɗin da zaka riƙa shiga saboda tsaro


Yana da kyau mu riƙa kula da kuma taka tsan-tsan da yadda muke amfani da wayoyinmu musamman wajen sauke applications da kuma shiga websites ko danna links ɗin da aka turo mana


 A yau akwai applications da suke É—auke da abinda ake kira da malware a turance, malware code ne da ake sakawa a cikin app wanda zai riÆ™a É—aukar bayanai daga cikin wayar mai amfani da wannan app É—in, za a iya amfani da bayanan a cutar da mutum a wayarsa ko kuma accounts nasa na social media ko kuma wasu accounts É—in na daban kamar na bankuna da sauran su, ko kuma ayi amfani da bayanan wajen yin wani abu daban, haka kuma akwai websites É—in da suma idan mutum ya shiga zasu iya É—aukar bayanansa, don haka sai a riÆ™a kula da manhajojin da za a riÆ™a saukewa akan waya da kuma shafukan da za a  riÆ™a shiga


Shawara ita ce ka riƙa sauke manhajoji daga playstore kai tsaye, domin manhajojin da aka sauke daga playstore sunfi tabbacin ingancin fiye da wanda za a sauke su daga wani website ko kuma a turama, idan babu manhaja a playstore to ka riƙa sauke manhajar daga asalin website ɗin masu manhajar, ma'ana dai ka riƙa sauke su daga wajen masu manhajar, saboda zaka iya zuwa ka sauke manhajar daga wani waje wanda zai zamanto ba asalin manhajar ka sauke ba kawai dai ka sauke irinta ne wacce aka kwafa kenan akayi cloning ɗin ta, irin wannan manhajar za a iya cutar da kai da ita.


Sannan ka riƙa shiga website ɗin da yake ɗauke da cikakken sunansa na asali kuma wanda yake da ma'ana, misali: https://www.instagram.com


Irin wannan website É—in da na bada misali da shi kana gani kasan shine asalin website É—in Instagram, amman idan kaga irin wannan sunan website É—in to ka sani fa cewa zai iya yiwuwa na macuta ne, ga misali kamar haka: https://www.instagram.followers.fddj.jd/ujs.get/instant.cuo


Irin wannan website ɗin ka guje su, sannan ka guji shiga website ɗin da ba ya ɗauke da https a farko sai dai http, ga misali nan a ƙasa:


https://www.wallpack.com

http://www.wallpack.com (a kula da irin wannan)


Don haka a riƙa kula sosai ƴan uwa.

Previous Post Next Post