Yanda ake hada application na wayar Android😍



Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da wannan lokacin ya kuke ya hakurin kasancewa tare damu a yau cikin shirin namu zamu kawo muku yadda ake hada App ne na wayoyin android harma da yadda mutum zai fara samun kudi dasu.


Sau da yawa mutane suna ganin an hada wani App wanda sai suji wannan app din ya birgesu sosai kuma suji suma suna sha'awar yin nasu da ace sun iya ko kuma sun san yadda ake hadawa.


Akwai tarin Apps yanzu da ake amfani dasu kuma mutum har yakai yana samun kudi dasu, kamar na karatu ko wakoki ko kuma game ko littattafai dadai sauransu wanda wadannan Apps din ana samu dasu sosai da sosai.



Wasu daga cikinmu sun san ana samun kudi dasu wasu kuma basu sani ba, sannan wasu koda suna son hadawa za kuga basu iya ba har sai sun kaiwa wasu sun basu kudi sannan su hada musu.


To yau munzo da wani App wanda idan kuka mallakeshi kuma zaku iya hada naku application din ta cikinsa kuma cikin sauki.

Kamar yan kasuwa masu son hada nasu App din da kuma sauransu duk zasu iya hadawa tanan idan sun mallaki wannan App din.

Bayan sun dora kayansu akai kuma zasu iya samun kudi dashi ta hanyar talla da ake dorawa akan kowanne irin App.

Kuma zaku iya dorashi a cikin play store ta inda mutane zasu iya daukowa.



Sannan zaku iya samun kudi sosai da wannan App din idan kuka kirkira ta hanyar dora masa talla idan kuka hada da admob kamar yadda ake yi.


Su admob din wani kamfani ne da suke bawa masu App talla kuma suna biyansu da daloli idan suka dora talla akan App din 


Dan haka zamu ajiye muku Link din wannan application din a kasa gurinda muka rubuta Download domin saukarwa


👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post