Yanda zaka dauki duk wayar da kake so a whatsapp SIRRI😘



Assalamu alaikum barkan mu da juma'a Ina mana tuni da mu karanta suratul kahfi da kuma yawaita salati ga fiyayyen Halitta ( S A W ) A wannan rana ta juma'a.

 

Yan'uwa yau ma wani application na kawo mana mai matuqar amfani wanda zai baka damar recorde din duk wata waya da kake yi a social media ko in ce duk wani chatting. 

Idan kun lura da kyu babu wata hanya da zaka iya record din duk wata waya da kake da wani idan ta whatsapp ne ko Imo ko Viber da sauran su. 

Hakan yasa na kawo mana wannan application wanda zai baka damar daukar duk wata waya da kake so kayi.

Akwai lokutan da zaka gani kana buqatar kayi record na wata waya mai matuqar amfani amman zakaga ta whatsapp aka kira ka ko kuma da ta Imo ko ta Facebook messenger.

To da zarar ka mallaki wannan application zai baka damar record din duk wayar da kake so ka ajje a matsayin sheda koda ace wata magana ce ta sirri kake so kayi record din.

Saboda haka kaje kasa zakaga na rubuta Download sai ka taba ka dakko application din a wayar ka.

Ga masu cewar basa gane yanda sukeyin amfani da dukkanin application da na kawo. Ku sani komai ya kasu kashi daban-daban idan kana son ganin dukkanin bayani akan application ko wani website to ka ziyarchi Youtube channel dina mai suna ( KK Techtube).

Ga link din app din a kasa

👇👇👇👇👇👇

 Download

Previous Post Next Post