Yanda zaka hana a bibiyi kiran ka. Koda wayar bata hannun ka.




Yanda zaka hana a bibiyi kiran ka. Koda wayar bata hannun ka.

Assalamu alaikum aminchin Allah a gareku yan'uwa na yau darasin da zamu tattauna akai shine. Wani application ne wanda zaka mallake shi sannan ya baka damar ka saka tsaro a dukkanin kiran wayar ka. Babu wanda zai qara dagama waya koda baka nan.

Wannan application amfanin sa shine. Zaka iya saita lokchin da inde an kira ka babu wanda zai iya daga ma waya koda a gida ne.

Saboda zakaga akwai wanda yana tsoron ya dinga ajje wayar sa a gida saboda gudun a kira shi matar sa ta daga ko yaran sa.

Kuma zaka ga dan kasuwa ne shi ko mai harkokin yau da kullum.

Amman koyaya aka kira shi zakaga matar shi ta daga. 

To idan ka saka wannan  application din a wayar ka. Shi application din zai baka damar ka saka security a dukkanin kiran wayar da yake shigo ma.

Nasan wani zai ce saboda yawan kiran shi da akeyi bazaiyiyu ace duk kiran da akayi masa sai ya saka security ba ko ince ya cire security sannan ya daga wannan wayar abin zaiyi yawa.

To application din ya baka damar saita wani adadi na lokachi wanda zaka saka acikin wayar ka iya dan wannan lokachin securityn zai dinga fitowa a duk wani kiran da akeyi maka.

Musali idan kana fita aiki ko kasuwa karfe 8:00 na safa sannan kana dawowa karfe 6:00 na yamma. 

Zaka iya saita wannan application din domin gudun idan ka dawo gida da yamma zuwa safiya saboda matar ka ko yaran ka kada su daga ma waya.

Zaka iya saitawa acikin application din misali daga wannan karfe 6:00 na yamma zuwa 8:00 na safe duk wani kira da za'a yi ma sai an saka security sannan zai bude.

Kaga  da zarar wannan lokachin yayi kawai wayar ka tana cikin security domin matar ka ko yaran ka l. Sannan batare sa ka kuma shan wuyar saita application din ba kawai idan 8:00 na safe yayi securityn zai daina bayyana a wayar taka.


Bugu da qari zaka iya saitawa duk wanai kira da akeyi ma sai an saka security sannan za'a daga shi. Sannan zaka iya saita iya wata number kawai domin idan aka kira da number ko nambobin da ka saita idan aka kira ka da su dole sai an saka security kiran zai dagu ko ince za'a iya daga kiran.

Wato shi wannan application gaskiya ya kamata ku mallake shi. Domin dayawa akwai wanda suke bibiya ta a youtube sun godemin sosai akan wannan application.

Saboda haka ku duba kasa zakaga na rubuta Download sai ka taba ahine zai baka damar sauke wannan application a wayar ka.

👇👇👇👇👇

 Downlod

Previous Post Next Post