Yanda zaka karanta sakon da aka goge a whatsapp



Assalamu alaikum barkan mu da wannan lokachi.

Cikin ikon Allah yau ma na kawo muku wani application mai amfanin amfanarwa. Saboda amfanin sa ne ma yasa banyi wata wata-wata ba na kawo muku shi domin ganin kunyi amfani a wayar ku.

Applicatiom ne zai baku damar karanta dukkanin wani sako da aka turo sannan aka goge shi musamman na whatsapp.

Na tabbata mutane da yawa suna buqatar wannan hanyar domin abinda yake damun su domin zakaga a whatsapp wani lokachin za'a turo da sako ko message sannan sai a goge wannan sakon. To babu wata hanya wadda zaka iya karanta wannan sakon sai de masu amfani da whatsapp GB sune zasu iya karantawa. Musamman idan mutum yana amfani da Normal whatsapp.

To wannan application din zai share muku kukan da kuka dade kuma jira. Domin idan kuka mallaki wannan application zai baku damar karanta dukkanin sakon da aka turo sannan aka goge shinkoda hoto ne ko video a whatsapp.

Sannan wannan application zai baka damar kare dukkanin wani app da yake turo ma da abin banza ta saman wayar ka.

Akwai application da suke turo da sakonnin banza ta saman waya. Amman idan ka mallaki wannan application zaka iya block din irin su.

Kaje kasa sakaga na ajje link din application din a wayar ka.

Zakaga na rubuta Download sai ka taba shine zai baka damar sauke application din a wayar ka.

Ga link din

 Download

Previous Post Next Post