Wayar ka tana shan Chaji ko wayan Daukar zafi? Ga wani application a wannan shekarar 2023

 Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu. Barkan mu da wannan lokachin. Ina yi muku fatan Alkhairi ya fama da wannan yanayi na sanyi😀. Musamman wanda ma basu da aure. 

Yan'uwa yau wani application na kawo mana mai matuqar muhimmanchi da ya kamata ka gaggauta mallkar sa. Domin zai baka damar kare kanka ga duk wata kafa da wayar ka take daukar zafi da kuma sha maka chajin da kake yawan yi a wayar ka.

Zan dan tattauna kadan akan wannan application din sannan a karshe zan baku shawarar yanda zaka tafiyar da wayar taka batare da kullum tana ta baka matsala ba.

Wannan application de ku duba kasa zaku ga link din sa a kasa sai kuje ku mallake shi domin nasan da yawan ku kun kalli cikakken videon bayanin application din cikin video. Acikin page na facebook dina duk da ma dai zan ajje muku videon a kasa sai ku danna ku kalla ga wanda bai kalla ba.

Ga videon kawai ka danna videon zai bude ma sai ka kalli cikakken videon ta nan.

👇👇👇👇



Dukkan wata waya da kuke amfani da kuma application da muke amfani da su suna da matsaloli sosai wanda inde ba an fada ma ba baza ka gane su ba.

Duk wani application da kake amfani da shi a wayar ka sun kasu kala video.

Akwai wanda normal sai ka bude su sannan zasu fara amfani da wayar ka bangaren sha maka DATA da kuma shan Chaji da duk wasu abubuwan da application din ka baka shi permission.

Amman akwai applications da yawan da koda tunda ka dakko su ka saka su a cikin wayar ka amman baka taba bude su ba to suna amfani acikin bayan wayar ka wato ( Background) To duk wata kafar da wannan application din yana yi bangaren sha maka chaji ko shan ye maka DATA ko daukar bayanan ka to fa zai dinga yi. Batare da ka sani ba.

Shi amfanin wannan application din zai binciko ma duk wani applicatiom da yake daukar bayanan ka ko shan chaji ko DATA sannan zai baka damar kashe shi ko ka bashi hutu hr sai ka taba shi sannan zaiyi amfani.

Shi yasa na binciko muku domin nasan akwai masu ire-iren matsalolin nan koda wayar ka tana rike ma chaji zaka wayi gari tana sha maka DATA ko wani abu da baka gane a kan wayar taka ba.

To kowace kalar matsala ce inde ka mallaki wannan application din normal wayar ka zata fara anfani da shi.

Nasan da yawan ku kun kalli videon domin ganin cikakken videon.

Kai ma ya kamata ka kalla saboda gane yanda amfanin sa yake.

               KARIN BAYANI

Da yawa mukan wayi gari wayoyin mu suna da matsalar da bamu san yanda zamu shawo kanta ba.

Kamar hakanan kana amfani da ita kawai sai wayar ta dauke ko ta kawo ta dauke. Ko ta dinga daukar zafi ko bata chaji da wuri da dai sauran matsalolin da muke ta fama da su.

Da farko de abinda ya kamata mu sani shine

Ya kamata mu dinga barin wayar mu tana hutawa. Misali a Rana koda na awa biyu ne. Ina nufin kana kashe ta tana hutawa gaba daya.

Ko a sati ka dinga bata hutu.

Ka sami chajar da tayi dai-dai da ita ba wadda tafita karfi ko bata kaita ba. Idan kaje siyan chajar kana tambayar irin wayar ka saboda gudun samun matsala. 

Akwai bayanai da yawa a baki na. Kawai na dan fada mana abinda suka fi addabar mu.

A kasa zaku ga na rubuta DOWNLOAD sai ka taba shine zaka sauke shi akan wayar ka.

👇👇👇👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post