Da wace waya kake amfani Android ko Iphone?. Ga yanda zaku dakko video kyut a kowace waya 2023

 Assalamu alaikum bayan dubunnan gaisuwa a gareku mabiya na dare da rana ina fatan kowa ina nan lafiya.

Yan'uwa duk de a cikin videon nafiyin bayani akan wayar iphone to shi wannan application din bama iya wayar iphone ba gaba daya duk mai amfani da kowace kalar waya android ko iphone din zaku iya amfani da wannan application domin dakko duk wani video daga youtube zuwa kan wayoyin ku.


Batare da kun sha wata wahala ba. Domin da yawa mukan buqachi mu dakko wani video da muka gani a youtube to dole sai de mu barshi tunda babu wani application takamaimai wanda google da kuma appstore suka yarda da shi.

Dukkanin wasu app da muke amfani da su wajen sauke kowane kalar video to basu da tabbas. Domin ire-iren su ne muke ta fadakar da yan'uwa wajen amfani da su.

Amman wannan application da na kawo muku kowane direct daga playstore ga masu amfani da wayar android zaku dakko shi masu amfani da kuma iphone zasu dakko a appstore.


Kada ku damu na ajje muku link din su gaba daya na kowace waya a kasa.

Amman zanyi muku bayanin yanda zakuyi amfani da shi a wayoyin ku.

Wato abin da zai baka mamaki da wannan application din shine. Bashi da nauyi sannan bashi da wani wahala wajen amfani da shi. Kawai da ka dakko link din video daga youtube zaka taba wajen wani madanni wanda daman gaba daya app din ma

kana bude shi madannin zaka gani. To shine idan wayar taka ta buqachi kaui paste go zata tambaye ka musamman masu amfani da iphone kana taba paste din nan to zakaga duk nauyin video zai sauka acikin yan sakanni sannan batare da yaja MB da yawa ba bayan nan bazai rage wa videon kyu ba ( quality).

Da farko de bayan ka bude application din zakaje daidai inda videon yake a youtube kamar haka.

👇👇👇👇👇


To zakaga Copy Link sai ka taba idan ka taba shine link din wannan videon zai copy.

Sai kaje ka bude application din da na baku 

👇👇👇



Sai ka taba daidai wajen dan ramin nan na tsakiya kawai tabawa zakayi bayan ka fito daga Youtube din kenan.

Kamar yanda na fada muku zai tambaye ku domin kuyi paste din wannan link din kamar hak kenan

👇👇👇👇


To sai ku taba rubutu na video wato ( Allow Paste ). Shine zai fara download amman zai yi muku talla acikin app din idan baku da hanyar kashe duk wata kafa da application yake yin talla.

Amman a lokachin tallan nan ma normal har ya fara download.

To kawai yana gama download din zai sauka akan wayar ku. 

Koda masu amfani da iphone zai sauka a wajen Photos batare da ka qara taba wani save ko download ba.

Idan kaje kasa zakaga na rubuta ( Iphone ) idan ka taba kan rubutun shine masu amfani da iphone zasu sauke wannan application din acikin wayar su.

Masu amfani da Android kuma Zakuga ( Android )  sai ku taba kan rubutun shine zaku sauke shi acikin wayar ku.

Wannan shine har amfani da wannan application mai abin mamaki da saukaka hanyar dakko kowane video daga youtube zuwa kan wayoyin ku batare da shan wahala ba.


Iphone

Android

Previous Post Next Post