Daga yau ka daina asarar kowane kudi a wayar ka 2023

Daga yau ka daina asarar kowane kudi a wayar ka 2023


Assalamu alaikum warahmatullah. Barkan mu da wannan lokachi na sanyi-sanyi kuma Zafi-zafi 😄😂. Wato ba mai gane lokachi sai wanda bashi da aure. Allah ka aurar damu ameen😄.



Yan'uwa yau darasin namu abinda ya danganchi sanin adadi na dukkanin kudin duniya ne baki daya. Akwai masu buqatar sanin launi ko yanayi na kowane kudi a kowane lokachi. Amman zakaga abin yana basu wahala. Koda ba masu hulda da kudi ba.  Akwai lokachin da zaka iya wayar gari kayi tafiya zuwa wata kasa ko kuma kudin kasar yazo hannun ka. Kna so ka daidai ta shi da kudin dake kasar ku domin sanin kima ko adadi na wannan kudin amman abin zakaga yana baka wahala. 

Idan kuma kaje wajen wani domin yayi ma bayani sai kaga Cuta ta shiga da hassada.

To dukkanin ire-iren wannan matsalar idan ka mallaki wannan application zai sauwake ma saukin sanin kowane kudi batare da kayi amfani da wani hanya mai wahala ba.

Shi wannan application ba iya adadin saka kudin da kake so ka sani bane A'A yana da abubuwa da yawan gaske da ya kamata ka iya.

Acikin wannan application zai baka damar sanin kudin wani kaya da zaka siya ko da ka siya daga wata kasa kuma a lokachin.


Misali ka shiga wani shago haka sai kaga kayan kuma ba a kasar ku bane. Sannan babu wanda zaka tambaya. Shi wannan application zaka iya daukar ko scan din wannan kudin na kowace kasa ne sai ka saita shi da kudin kasar da kake so ka sani. To zai fada ma akan nawa wannan kaya ya kama a kudin kasar ka.



Abinda zai baka mamaki da wannan application din idan ka tashi convert ko chanja kudin da kake so baya wani buqatar dole sai kankunna data. 

Kawai da ka saita adadin kudin kasar da kake so kasan nawa ne sai a kasa zai baka damar saka kudin kasar ku. A dan kankamen lokachi zai fada muku nawa ne kudin ya kama a wannan lokachin.


Sannan koda ma ace kana so ka gane a wannan lokachin akan mawa Dollar ko CF take  idan ka shigo wannan application din zakaga jerin kudeden duniya da kuma akan nawa suke a kudin kasa ku.


Ku mallaki wannan application mai matuqar muhimmanchin gaske.

Kuje kasa zakuga na rubuta Download da koren rubutu sai kuntaba shine zai baki damar sauke wannan application a cikin wayoyin ku.

Domin fara amfani da shi.


Download

Previous Post Next Post