Daga yau ka daina Rasa (missing) Din whatsapp din ka Iphone ko Android koda GB ne

 


Assalamu alaikum barkan mu da wannan lokachi ya fama da juriyar hakuri da bibiyayar mu. Muna godiya. Yawan bibiyar da kuke mana shi yake sakawa muke nemo muku applications masu amfanin gaske da abin mamaki.

Yau wani application na kawo mana wanda zai baka damar tura duk chat din ka na whatsapp daga iphone zuwa android ko daga android zuwa iphone. 


Sanin duk wani mai amfani da daya daga cikin wayoyin da na lissafo na Android ko iphone din babu damar yin transfer na chatting din whatsapp daga iphone ko android din. Saboda koda ma baka sani ba to bari na dan tunatar da kai.

Ita wayar Android duk wani chatting da kake kuma kana Backup din wannan chat din na whatsapp to yana zaunawa ne a Google Drive saboda dole ne ma idan zaka ajje ko backup din chatting din sai ka saka Gmail din ka. 

Ita kuma wayar iphone duk mai chat a whatsapp kuma yana ajje chatting din sa. Wato backup to yana zaunawa ne a iCloud. hakan yake sawa ma inde icloud din ka ya cika baka da damar qara ajje duk wasu abubuwa naka koda chat din whatsapp din ne.

To hakan yake sawa inde kana amfani da Android kuma ka chanja waya iphone ba damar dawo da chatting din ka zuwa google drive din ko icloud din. Saboda kowace waya akwai abinda take dauka. Dole ne iphone icloud take dauka. Ita kuma android Google drive kadai take dauka. 

To shi wannan application din zai baka damar dawo da duk chatting din ka na whatsapp daga kowace waya android din ko iphone din.

Download

 << MENENE BACKUP?>>

Backup hanya ce da zaka ajje duk abubuwan da kake so a wani application sannan zaka saka gmail ko wani abu da ya danganchi haka. Daga baya koda ka chanja waya ko wayar ta sami matsala kawai da zarar ka dakko irin wannan application din kuma ka saka gmail din da kayi amfani da shi a dayar wayar shine zai baka damar Restore din duk abubuwan da ke cikin tsohuwar wayar taka.

 Whatsapp backup yana daya daga cikin abu mahimmi wanda ya kamata muna kunna shi. Saboda gudun chanja waya bayan nan zaka iya saitawa wane lokachi zuwa wane loakachi zai dinga ajje ma wannan chatting din da kake. Misali kullum ko kuma duk sati ko duk wata bayan ka saita zai tambaye ka dame dame kake so ya dinga ajje ma. Misali normal chat ko harda Hoto ko videos da kuma Decument dukkanin abinda ka zaba shine zai baka damar ajje maka komai amman adadin abubuwan da ka zaba adadin shan DATA da kuma shan Storage na kan Google drive da kuma Icloud din ka.

A takaice de wannan application amfanin sa shine kayi transfer din duk wani chat din da kayi daga iphone ko daga android ko nace daga Google drive zuwa iCloud.

Sannan shi wannan application baya wani buqatar Internet yana da saurin gaske wajen turawa.

Bugu da qari zaka iya transfer din duk wani kayayyakin da daga tsohuwar wayar ka zuwa sabuwar da ka chanja bama iya chatting na whatsapp ba.

Zakaga na ajje link din a kasa na rubuta Download da koren rubutu sai ka taba shine zai baka damar saukewa a akan wayar ka.

Download

Previous Post Next Post