Wannan Application din ne kawai mafita a kowace waya 2023 ( Iphone & Android)

Wannan Application din ne kawai mafita a kowace waya 2023 ( Iphone & Android)



Assalamu alaikum barkan mu da safiya ina fatan mun wayi gari lafiya.

A gurguje wani application ne da na kawo mana zai fada maka duk wata matsalar dake cikin wayar ka. Amfanin irin wadannan application din sune.

Da yawa zaka iya ganin waya wajen abokin ka ko kuma kaje kasuwa ka sayi waya musamman irin wadda aka fara amfani da ita. 



Idan har ka sami mutumin kirki shine zai iya baka wani adadi na kwanaki ko na awanni wanda zaka iya gwada wayar kaga matsalar ta sannan ka fada masa idan akwai matsala haka.

To matsalar da ke faruwa zaka iya wuce wannan adadin da ya baka amman a lokachin bazaka iya ganin kowace kalar matsala ba. sai bayan yan kwanaki sai kaga wayar tana da wata matsala haka. 

To idan ka mallaki wannan application da na kawo muku a kowace kalar waya koda ma a daudai inda zaka sayi wayar ne zaka iya saka application din sai duba komai na matsalar wayar.

Tun ma kafin kuyi ciniki.



Abu na biyu kai kanka da kake amfani da wayar a halin yanzu wata qila tana baka wata matsala kuma ka rasa meke faruwa wata qila ma har mai gyara ka kaiwa amman bai gane matsalar ba.

To idan ka saka wannan application din kuma kayi amfani da shi zai fada ma duk matsalar wayar ka.



Kowace kalar waya iphone ko Amdroid dukkanin su zaka iya amfani da application din.

Wato abinda zai baka mamaki da wannan application shine. koda abinda ya danganchi karar speaker wayar da kuma blirtooth da network da duk wani bangarori na screen din wayar duk zaka iya dubawa ta cikin sa.

Indw zaka iya hakuri kabi daki-daki wajen bude kowane fanni na cikin application din to shi zai fada ma duk komai lafiya yake ko ba lafiya yake ba.



Misali idan kazo fannin network ka gana ciccike komai a karahe idan ka dannan Done shi application fin da kansa zai ce ma wannan bangaren lafiya yake ko kuma ba lafiya yake ba. Haka bangaren screen da kuma battery da dai sauran su.

Wato de na tabbata daga dan karanta wannan rubutu kun gane amfanin wannan application.

Sai ma kun saka shi acikin wayar ku sannan zaku gane amfanin sa.



Duk kowace kalar waya iphone ko Android zan ajje muku link din kowace a kasa sai ku ta a ku dakko application din.

Idan kaje kasa kaga an rubuta Iphone da koren rubutu to wannan application din na wayar iphone ne to masu irin wayar ne zasu taba dai su dakko.

Idan kuma kaga an rubuta Android wannan kuma na wayar Amdroid ce kowace kala kawai sai ka taba ka dakko application din.

Bayan nan kada ku manta da turawa yan'uwa wannan darasi domin su dakko wannan application mai muhimmanchi.

 Iphone

iphone

Android 

Android

Previous Post Next Post