Wannan application din zai baka komai kyuta koda na kudi ne 2023




Assalamu alaikum ina muku fatan Alkhairi. Ya kowa da kowa ina fatan de kowa yana lafiya. Yan'uwa yau darasin mu akan wani application ne mai matuqar muhimmanchin da ya kamata ku mallake shi. Kamar yanda kukaji bayani acikin videon shine wannan application zai baka damar daukar fuskar wani hoto na wani application wanda acikin application din ba'a ba da damar dauka ba ( Screenshot ). 

Nasan wasu basu fahimchi bayanin ba. Amman ku biyo mu a sannu zan muku cikakken bayani insha Allah.

Da yawa akwai application da basa bayar da damar ayi screenshot acikin bama iya application ba akwai wasu website ma haka. Kamar irin wasu application na banki ko na wani kallo haka kamar irin su Netflix ko wani application da ake biyan kudi.

To amfanin wannan application din shine zai baka damar kayi screenshot na kowane kalar application sannan kayi amfani da shi a wayar ka. 

Zaka iya buqatar ka dauki fuskar gurin domin wani muhimmin abu haka amman zakaga shi application din ko website din bai ba da damar yin hakan ba.

Kamar wani application na banki wanda kake so ka nunawa wani transfer na kudi haka ko wani history. To direct zaka iya ascreenshot din sa.

Bayan nan ba iya wannan bane amfanin wannan application din ba. Zai iya fassara ma dukkanin wasu yare kuma ya karanta maka. Da zarar kazo daidai inda kake so ya karanta ma kawai zaka saita application din sannan ya karanta maka. 

Akwai wajen duba dukkanin abubuwan da kake so ( Search engine) kenan kamar Google.

Akwai abubuwa da yawa wanda sai ka saka wannan application din a wayar ka sannan zakaga sauran ayyukan nasa.

Asali idan ka dakko application din a wayar ka zai fito a jikin screen din wayar taka sannan zakayi control din duk wani abu da kake so kayi amfani da shi.

Idan ka zo kasa zakaga na rubuta Download da koren rubutu sai ka taba ka sauke application din a wayar ka sannan kayi amfani da shi.

👇👇👇👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post