Yanda ake bude eNaira a kowace waya Android da kuma iphone 2023

 Assalamu alaikum yan'uwana barkan mu da wannan lokachi. Allah yasa mudace. Ameen

Yan'uwa duba da abubuwan da mutane suke ta korafi akai ta maganar eNaira. Akwai da yawa suna buqatar su san yanda ake amfani ko bude wannan Wallet ko Application na eNaira.

To da yardar mai duka ubangijin sammai da kassai zan dan kokarta na yi muku bayanin yanda ake bude wannan application na eNaira.

Bayan nan akwai video na musamman wanda zanyi muku yanda ake amfani da shi da kuma muhimmanchin sa.

Da farko de duk masu amfani da wayar Android da iPhone na ajje muku link din Application din a kasa sai kuje ku dakko shi.

Bayan ka dakko zamu fara darasin daki-daki insha Allah.

Da farko bayan ka bude Application din kamar yanda zan nuna muku acikin hoton da yake kasa.

👇👇👇👇👇👇



Bayan ka bude application din idan kukayi la'akari da hoton sama zaku ga ( Create Wallet ) inda na zagaye kenan. To sai ka taba.

Idan ka taba zai nune ma kamar yanda hoton kasa yake.

👇👇👇👇


To zakuga a hoton sama akwai ( Individual Wallet ) Sannan akwai ( Business Wallet ) Anan banbanchin su shine.

( Individual)shine normal kowa wanda zai bude idan kuma ka zabi ( Business) To na kasuwanchi kenan kamar kana da wani shago zaka budewa shagon naka shine zaka taba business din.

Amman idan normal naka ne sai ka taba Individual saboda haka nima Individual din zan taba.

To kaima kawai ka taba ( Individual din ) sannan zaka ga Continue a kasa a jikin hoton kenan wanda na ajje muku.

Bayan ka taba Continue din zai nuno ma kamar haka a hoton kasa kenan.

👇👇👇👇




Bayan ya bude ma kamar yanda na nuno muku a hoton sama zaku ga na cike komai.

A farko zakuga na saka number ta Amman na cire ( 0 ) Farko to sai ka zuba kamar yanda nima na saka.

Amman Afwa dan Allah kada ku kira wannan number da kuka gani a jikin hoton.

Bayan nan a gidan kasa zakuga ance ku rubuta Password to sai rubuta irin misalin da nayi muku a jikin hoton zakuga nayi amfani da Symbol da kuma Alph. Da Num da kuma Capital Letter. Idan kana rubutawa zakaga a kasan inda password din yake yana komawa Kore. Nayi amfani da Symbol wato ( @ ) Sannan nayi amfani da Capital letter wato ( A ) Sannan nayi amfani da Number wato (2023) Shine ya zama (@Abubakar2023) Sannan ana buqatar password din ya wuce 12 zuwa sama ko kuma 12  daidai. To kaima abinda zakayi amfani da shi kenan. Ina fatan kun fahimchi yanda password din yake.

Bayan nan a kasa zaka ga dan wani akwatu dan karami sai ka cike shi. Kamar de Daidai da yanda nayi acikin hoton saman da na dora muku. 

Bayan nan sai ka taba Continue sai ka taba. 

Idan ka taba shine zai nuno maka yanda hoton kasa yake.

👇👇👇👇👇👇👇




Zasu turo ma da OTP ta number da ka saka to sai kazo daidai inda gurbin nan yake sai ka zuba su sannan ka taba continue.

Bayan ka taba continue shine zai nuno ma kamarbyanda hotoj kasanyake.

👇👇👇👇👇👇



Zakuga ya nuno muku kamar yanda kuka ga Form na hoton sama kenan.

Sannan zakuga komai na cike shi sai kuyi amfani da form din wajen cike naku.

Sai de karin bayani akan ( Residence ) Da kuma (Origin). Idan kazo abinda ya danganchi State ko Country Idan a gaba kukaga Residence shine ana nufin inda kuke zama a halin yanzu kenan idan kuma kuka ga State da kuma Country amman a gaba zakuga Origin yana nufin asalin inda mahaifar ka take.

To idan kuka gama cikewa sai ku taba Continue.

Bayan nan zai nuno muku kamar yanda hoton kasa yake.

👇👇👇👇👇👇


Bayan nan shima sai ka taba Continue. Domin akwai sauran cike-Cike.


Shine zai nuno ma haka. To anan abinda zakayi shine.

Daman Tun farko mun kirkiri password wanda muka saka guda 12 nan har nayi muku bayani a farko.

Sai ID ne zamu nemo.

Shi kuma ID din zasu tura ma da message ta number da ka bude sai kaje message din. Ka nemo ID din.




Acikin message din da suka tura muku zakuga Wallet ID: Kamar yanda na gewaye da JAN abu a hoton sama kenan.

To wannan Numbobin zaka kwafa sai kaje inda na nuno muku hoton biyu kafin wannan kennan.

Amman ka misalin sa a kasa.

👇👇👇👇👇


Sai ka saka Wallet ID wanda suka turama a message sannan sai ka saka Password din ka saka a farkon bude application din wanda nayi muku misalin sa.

To bayan nan zakaga ( LOGIN ) Sai ka taba.

Bayan ka taba LOGIN zaka ga ya nunoma wani form daban kamar yanda zanyi muku misalin sa a hoton kasa.

👇👇👇👇


Bayan nan sai ka taba (Setup) Kamar yanda ya nuno a hoton sama kenan.


Shine zai budema kamar haka. Zai baka damar ka kirkiri PIN wanda idan kantashi tura kudi ta cikin wannan wallet din dole sai ka saka PIN din. Kuma pin din guda (4) ne misali 1234 Amman sai ka zabi wanda bazaiyi sauki ba.

Sannan a kasa zakaga Password to sai ka saka Password din da kake bude application din wannan de wanda na koya muku har ka kirkiri kuma da shi ka bude app din.

Bayan ka gama sai ka taba Continue.


Shine zai nuno ma Success kamar yanda ya nunomin a Hoton sama. Sai ka taba Continue.


Shikenan ka bude waller ko Application na eNaira. Kawai zakaga Receive da kuma PAY.

Sai a saura Darasin mu zanyi bayani akan yanda ake turawa da kuma karba.

Kada ku manta da Turawa yan'uwa domin suma su bude wannan Wallet.

Ga link din duka App din na wayar iphone da kuma Android Sai ku taba ku dakko su.

Zakuga idan Android ne zakuga na rubuta sunan da koren Rubutu sai ka taba ka dakko na wayar Android idan kuma na iphone ne zakuga na rubuta iphone shima kana tabawa zaka dakko na wayar iphone.

#NAGODE

Android

Iphone



Previous Post Next Post