Yanda zaka browsing batare da an dauki bayanan ka ba

 Yanda zaka browsing batare da an dauki bayanan ka ba.

Nasan wasu zasuyi mamakin wannan darasin. Afwa amman kafin nan ina muku sallama Assalamu alaikum barkan mu da sake saduwa a sabon darasin namu.

Da yawa bu sani ba muna shiga wasu website ko wata browser tana daukar bayanan wayoyin mu bamu sani ba. Ko kuma idan mun ziyarchi wani website din zakaga yana turo mana da tallolin batsa ko ya takurawa wayar ka.

Ga yanda fuskar browser take

👇👇👇👇



To matsalar da take faruwa anan shine. Wani lokachin muna amfani da browser ne wadda gaba daya bata da wani sirri kuma bata da Amana domin zata iya ba da bayanan ka zuwa duk website din da ya buqachi hakan ko kuma itama da kanta ta dauka kai kuma duk baka sani ba.

Tabbas ya kamata mu dinga lura wajen tantance wace browser zamuyi amfani da su acikin wayoyin mu.

Hakan yasa na kawo mana wata browser da zata bamu damar kare dukkanin wani bayanan da yake acikin wayar mu. 

Zata datse duk wani website da ka ziyarta idan zai bawa wayar ka matsala ko zai dauki bayanan ka. Sannan itama da kanga akwai tsaro sosai acikin ta.



A gaskiya bazan boye muku ba duk browser da nake amfani da ita inde a wayar android ne to ona amfani da wannan browser da kuma Chrome. Duk da de wasu nasan zasuyi zirgin chrome din nake ta bayani akan ta haka. AA ba chrome bace. Duk de da ita chrome din itama akwai tsaron da take da shi.

Amman bata da abubuwan da zata qarama tsaro acikin wayar ka da sirrin ka baki daya.

Bugu da qari wannan browser akwai VPN wanda zai baka damar boye asalin inda kake da zama. 

MISALI!.     Idan kana son ka ziyarchi wani website amman kana tsoron zasu gane asalin inda kake to zakayi amfani da VPN ka chanja kasa baki daya sannan idan ka chnja kuma ka shiga website din zasu ga alamar a asalin VPN din da ka chanja.



Bayan nan akwai website da bazasu bada damar ka ziyarta ba ko ka dakko wani abu ba ko kuma idan ka shiga zasu bak asalin yaren da bazaka gane shi ba.

To inde kayi amfani da VPN kuma ka saka wata kasar to zasuyi amfani da wannan kasar sannan su baka damar ziyarta har ka dakko abinda kake so ko ka bude account da shi ko kuma su baka wannan yaren kasar da ka ziyarta.

Sannan ita wannan browser din akwai BLOCK ads acikin bi ma'ana zaka kulle duk wata talla da yake a cikin wani website musamman na dakko video ko film ko wata software wadda zaka gansu suna da yawan talla sosai.

Sannan koda ace ka danna wannan block ads din akwai website din da idan ka ziyar ce su to asalin wannan programing din da sukayi amfani da shi zasu saka talla a matsayin JAVASCRIPT wanda ba duk wani app ko browser bane yake blocking din tallan. Amman ita wannan browser zata block duk wata kafa ta talla a kowane website.



Sannan zata fada maka adadin tallolin da tayi block gaskiya ya kamata ku mallaki wannan browser musamman masu yawan bincike a website.

Idan kaje wani website zaka dakko wani abu na video ko software ko application ko pdf ko dai wani abu haka. To shi wannan website din may be na karya ne inde ka danna download to zaizo a matsayin VIRUS ne zai bawa wayar ka matsala ko computer ka. Zakaga ta maqale ko tana mutuwa da kanta ko kaga videos ko hotuna basa budewa har sai ka biya wadannan website din kudi sannan zasu cire maka ko kuma kayi wa wayar taka Restore ko computer Format.

Kuje kasa zan ajje link din wannan browser domin ku sauke su acikin wayoyin ku.

Sannan akwai abubuwa da dama wanda ban lissafo ba.

Amman idan kun mallake ta normal zakuyi amfani da ita

👇👇👇👇👇👇

Download

Download

Previous Post Next Post