Yanda zaka dawo da abubuwan da ka boye a wani application 2023

 


Assalamu alaikum barkan mu da safiya ya kuma dan sanyi-sanyi. 

Yau na kawo mana wani application wanda da yawa ana ta qorafi akan ire-iren su shi yasa na zabi mana wanda ya dace muyi amfani da shi.

Application wanda yake bamu damar boye hotuna ko videos wanda bama so kowa yana ganin su. To amman matsalar da ke faruwa da irin wadannan application din shine. Wat rana sai ka zuba hotunan ka ko videos din ka kawai sai wayar taka ta sami matsala ko kuma haka nan idan ka shiga application din ka nemi wadannan abubuwan da ka zuba ka rasa.

To wannan application din zai baka damar zuba abubuwan ka gaba daya sannan koda ace idan sun bata ko ka neme su ka rasa zaka iya dawowa da komai batare da ka rasa abubuwan naka ba.

Ya kamata ka mallaki wannan application mai abin mamaki.

Daman tun asali idan ka dakko application zaka saka Gmail din ka acikin application din saboda shine zai baka damar dawowa da abubuwan naka.

Koda ka chanja waya sannan koda ka chanja application din.

Da zarar ka dakko application din sannan ka saka gmail din shine zaka dawo da abubuwan da ka saka a tsohuwar wayar taka.

Ga link din application din anan kasa zaka ga na rubuta Download da koren rubutu idan ka taba shine zai baka damar sauke application din a wayar ka

👇👇👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post