Yanda zaka gano wanda yake bibiyar sirrin wayar ka 2023

Yanda zaka gano wanda yake bibiyar sirrin wayar ka 2023



Assalamu alaikum ina muku fatan alkhairi. Yan'uwa videon mu na yau zai baka damar gano dukkanin wani application da aka saka maka yana daukar bayanan ka baka sani ba.

Abinda ya danganchi kiran waya ko daukar video ko hotunan ka. Da yawa akm iya saka mana wasu application ko kuma wayar ta zo da shi. To idan ka saka wannan application din zai baka damar binciko duk wani app da yake daukar bayanan ka.

Da yawa nasan wasu zasuyi mamakin wannan darasin amman wasu zasu ce tabbas suna zargin ana bibiyar duk wani kira da sukeyi. Ko kuma daukar wani bayanan su musamman hotuna ko video amman basu san ta wace hanya ake bi ba.

To tabbas koda kana zargin hakam ka gwada wannan application shine zai tabbatar ma da abinda kake zargi. Domin zai nunama duk wani application da yake bawa wayar ka matsala koda an boye shi.

Da farko de idan ka dakko wannan application din gaba daya babu wata wahala wajen saita shi.

To bayan ka bude application din zakaga bangarori da dama to sai kabi daya bayan daya ka bude shi.

To duk wani app da aka boye a backgroud din wayar ka zai bayyana. 

Sannan bayyanar ba wai acikin wayar ka zaka ganshi ba aa acikin application din.

Sai de ta cikin application din zai baka damar cire wannan app da baka san da shi ba.

Kaje kasa zakaga na rubuta Download da zarar ka taba shi shine zai baka damar sauke application din a wayar ka.

👇👇👇👇👇

Download

Download

Post a Comment

Previous Post Next Post